Bayan Barin Kujerar APC, Hadimin Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Son Kai
- Tsohon hadimin Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya yi magana kan adalci da rabon dukiya a jihohi
- Yakasai ya yi zargin cewa an ware biliyoyin Naira domin ayyuka a jihar Legas cikin shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu
- Hakan na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin nuna bambanci tsakanin yankunan Najeriya wajen yin ayyuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Ana cigaba da bayyana ra'ayoyi game da ayyukan da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta fi mayar da hankali a kansu.
Tsohon hadimin Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai ya yi zargin cewa an kashe makudan kudi wajen ayyuka a Lagos, yayin da jihohi kamar Kano ke fama da karancin ayyuka.

Source: Facebook
Tsohon hadimin ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar, 02 ga Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yakasai ya nuna damuwa kan yadda irin wannan rabo zai iya haddasa rashin adalci wajen ci gaban kasa, inda ya tambaya ko Tinubu shugaban kasar Najeriya ne ko na Legas.
Yakasai ya zargi Tinubu da nuna wariya
Salihu Tanko Yakasai ya lissafa wasu daga cikin manyan ayyukan da aka kaddamar a Legas, ciki har da:
- Hanyar Lagos–Calabar
- Hanyar Lagos–Ibadan
- Gyaran filin jirgin saman Murtala Muhammed
Har ila yau, ya ce akwai ayyuka kamar kamar hanyar Lagos–Shagamu, hanyar Lekki–Epe, da tsawaita hanyoyi kamar Lagos–Badagry zuwa Sokoto da makamantan su.
Punch ta rahoto cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware makudan kudi har N712bn domin gyara filin jirgin saman Murtala da ke Legas.
Lamarin ya jawo suka daga Arewacin Najeriya lura da cewa ba a ware kudin kamar su ba a wasu jihohin da za a yi gyaran filayen jiragen sama.
Sai dai duk da haka, a kwanakin baya, ministan ayyuka na kasa, David Umahi ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana yi wa kowane yanki na Najeriya adalci.

Source: Facebook
Maganar adalci a tsakanin jihohi
Yakasai ya yi tambaya ko irin wadannan manyan ayyuka da ake a Legas za su kasance a jihohi kamar Kano, inda ake ganin ana yin ayyuka kadan.
Ya nuna cewa zamantakewa da adalci suka kamata su kasance a farkon shugabanci, ba wai bambanci ba ga jiha ko kabila.
Hadimin Ganduje, ya bayyana cewa akwai bukatar yin irin ayyukan a kowace jihar domin tabbatar da adalci.
A makon da ya wuce ma dai sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi korafi da cewa shugaban kasar Bola Tinubu yana ware Arewa wajen yin ayyukan raya kasa.
Da yake magana a tsakiyar makon nan, Yakasai wanda ya nemi takarar gwamnan Kano a zaben 2023 ya nuna akwai abin dubawa a zancen Kwankwaso.
BUK: Tinubu ya canza Gawuna da Kaita
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sauke tsohon dan takarar gwamnan Kano, Nasiru Gawuna daga shugabancin kwamitin gudanarwa a jami'ar BUK.
Legit Hausa ta rahoto cewa shugaba Bola Tinubu ya maye gurbin Nasiru Gawuna da Sadiq Kaita a ranar Juma'ar da ta gabata.
Nasir Gawuna dai ya kasance tsohon mataimakin gwamnan Kano karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma ya nemi gwamna a 2023 bai samu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


