Canjin kudi, Kanu, ASUU da Abubuwa 5 da Tinubu Zai Ci Karo da Su da Ya Shiga Aso Rock

Canjin kudi, Kanu, ASUU da Abubuwa 5 da Tinubu Zai Ci Karo da Su da Ya Shiga Aso Rock

  • A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Asiwaju Bola Tinubu zai hau kan kujerar Shugaban Najeriya
  • Akwai muhimman abubuwan da suke jiran zababben shugaban kasar a yayin da ya shiga Aso Rock
  • Ana jiran Bola Tinubu ya inganta tattalin arziki, ya hada-kan al’umma, kuma ya tabbatar da tsaro

1. Canjin kudi

Kusan babban abin da Bola Tinubu zai nemi ya fara gyarawa shi ne tsarin canjin kudi da babban bankin CBN ya yi wanda ya jefa kusan kowa a cikin mawuyacin hali.

Ana sa ran Gwamnatin Tinubu da bankin CBN zai sake yi wa tsarin kallo na dabam musamman ganin kotun koli ta ce a cigaba da kashe tsofaffin N500 da N1000.

2. Tallafin man fetur

Daga ranar da Bola Tinubu zai karbi mulki, an ji labari babu mamaki farashin fetur ya karu domin Ministan tsare-tsare da kasafi ya ce za a janye tallafi bayan Mayu.

Kara karanta wannan

Farashin Man Fetur Zai Lula, Gwamnatin Tarayya Tana Shirin Barin Tinubu da Jan Aiki

Ministan tsare-tsaren kasa da kasafi ya ce ana jiran aikin kwamitin Farfesa Yemi Osinbajo kafin gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauki matsaya kan batun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

3. Nada mukamai

Jama’a za su zura ido domin ganin wadanda Bola Tinubu zai tafi da su. Ministoci da sauran manyan mukarraban da za a nada su na da matukar tasiri a gwamnati.

Baya ga haka akwai sauran muhimman mukamai a hukumomi da ma’aikatu da hafsoshin tsaro da tirka-tirkar wanda zai zama Sufeta Janar na ‘Yan Sanda.

4. ‘Yan adawa

Akwai yiwuwar gwamnati mai zuwa ta dauko ‘yan hamayya ta ba su mukamai domin adawa ta lafa. A baya, Ummaru Yar’adua ya yi mulki da 'yan adawa.

Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima a Borno Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

PM News ta rahoto cewa irinsu Abdullahi Ganduje, Atiku Bagudu, Abubakar Badaru, Abdullahi Sule da Nuhu Ribadu sun fara kokarin lallashin Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

A dakatar da shi: Hadimin Tinubu Ya Bukaci Buhari Ya Dauki Mataki Kan Gwamnan CBN

5. Matsin lambar tattalin arziki

Tattalin arzikin Najeriya yana cikin mummunan yanayi a yau, ‘Yan Najeriya za su rai gwamnatin Tinubu ta kawo karshen tsadar rayuwa da yunwa da ake fama da su.

6. ASUU

Abubuwa za su canza a jami’o’in tarayya a gwamnatin da za ta karbi mulki. Ana bukatar daina yajin-aiki kuma malamai su na neman albashin watanni takwas.

7. Tabbatar da zaman lafiya

Cibiyar CEDDERT tayi ikirarin akwai gungu fiye da 80 na ‘yan bindiga a Najeriya baya ga ‘Yan IPOB da ke yankin Kudu, dole ne Tinubu ya dage wajen inganta tsaro.

A wannan gaba, zai yi kyau a nemi yadda za a kawo karshen rikicin Nnamdi Kanu da Najeriya. Hakan zai iya faranta ran mutanen yankin Kudu maso gabas.

8. Muslim-Muslim

Tikitin Musulmi da Musulmi ya jawo wasu kiristoci sun ki zabensa a Fubrairu, akwai bukatar ya nuna zargin da ake yi masa na fifita wasu ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Abokin Gamin Atiku Ya Roki 'Yan Najeriya, Ya Maida Martani Kan Ci Gaba da Amfani da Tsoffin N500 da N1000

Asali: Legit.ng

Online view pixel