Kurunkus: Wike Ya Fadi Matsayarsa kan Masu Marawa Tinubu Baya
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan masu marawa Shugaba Bola Tinubu baya
- Wike ya bayyana cewa yana tare da duk wanda yake nuna goyon baya ga shugaban kasan Najeriya
- Ministan ya nuna cewa baya la'akari da jam'iyyar mutum, indai yana goyon bayan Tinubu, tabbas yana tare da shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya bayyana cewa zai goyi bayan duk wanda ya mara wa Shugaba Bola Tinubu baya.
Wike ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis yayin da yake yabawa tsohon sanatan Abuja, Sanata Philip Aduda, da kuma shugaban karamar hukumar AMAC, Christopher Maikalangu.

Source: Twitter
Wike ya hadu da tsohon Sanatan Abuja
Jaridar Leadership ta ce ya yaba musu ne a lokacin kaddamar da aikin samar da ruwa a yankin Karu da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya jinjina wa mutanen biyu bisa kwarewarsu da kuma kokarinsu na kawo ci gaba ga jama’a.
Nyesom Wike ya yi alkawarin gina hanya mai tsawom kilomita biyu a yankin Karu, rahoton The Nation ya tabbatar.
Wike ya jaddada cewa zai marawa waɗanda ke ci gaba da mara wa gwamnatin Tinubu baya, inda ya kuma yi kira ga jama’a da su nuna goyon baya ga waɗanda gwamnati za ta saurara.
Ya ce Maikalangu mutum ne mai kwazo da himma sosai wanda ya yi amfani da damar da yake da ita wajen kawo ayyuka da dama ga jama’arsa a karamar hukumar.
Wike ya kara da cewa idan Maikalangu ya sake lashe zaɓen shugaban karamar hukumar AMAC, gwamnatinsa za ta yi masa duk abin da ya nema.
Abin da Wike ya fadawa Maikalangu
"Ina nan ne domin na yi magana kan waɗanda ke da dama wajen shiga gwamnati domin kawo wa jama’a ci gaba."

Kara karanta wannan
Tsohon ministan Buhari ya yi magana game da mulki, 'yan adawa da halin da APC take ciki
"Shugaban karamar hukuma yana da dama a wajenmu. Duk abin da ya faɗa mana, za mu yi. Shi kaɗai ne mutum ɗaya da na sani. Idan ya sake lashe kujerar shugaban AMAC, za mu bashi duk abin da yake bukata."
"Ban san jam’iyyar da yake ciki ba, amma na san yana tare da Tinubu. Duk wanda ya mara wa Tinubu baya, ni ma zan mara masa baya."
- Nyesom Wike

Source: Twitter
Yadda Wike ya jinjinawa gwamnatin Tinubu
Ministan ya kuma jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta cika alkawarinta na samar da ruwan sha mai tsafta ga garuruwan da ke wajen birni, wanda gwamnatocin baya suka kasa cimmawa a yankin Karu.
"Mun taɓa samun gwamnati da ta shafe shekaru biyar a nan, ko ba haka ba? Mun taɓa samun gwamnati da ta shafe shekaru takwas a nan, ko ba haka ba? Shin akwai wata gwamnati da ta zo ta ce za ta samar muku da ruwa? Kun taɓa samun ruwa a baya?"
"Wannan gwamnatin ta yi muku alkawarin samar da ruwa, ko ba haka ba? To yanzu mun zo mun cika muku alkawari. Za ku tuna da waɗanda suka samu dama amma suka ki yi muku komai? Za ku tuna da waɗanda suka bar Karu babu kulawa, za ku tuna da su?"
"To ga mu nan mun zo domin mu tabbatar da cewa kun samu ruwan sha mai tsafta kamar yadda muka yi muku alƙawari.”
- Nyesom Wike
Gwamnatin Najeriya ta maido shirin GEEP
Labari ya gabata cewa an dawo da shirin GEEP, kuma an canza masa suna zuwa RHGEEP 3.0 a karkashin jagorancin Mai girma Bola Ahmed Tinubu.
Wannan shiri yana taimakawa yan Najeriya musamman talakawa da tallafin kudi ko bashi kamar yadda aka sani tun a gwamnatin da ta gabata.
Gwamnatin Tinubu ta fitar da tsare-tsaren yadda mutane miliyan biyar za su shiga shirin kwanaki bayan an fito da shirin taimakawa iyaye da kudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

