Wike Ya Sacewa Amaechi Gwiwa kan Yin Takara da Tinubu a 2027
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sutule Rotimi Chibuike Amaechi kan burinsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2027
- Nyesom Wike ya bayyana cewa tsohon ministan sufurin ba zai kai labari ba, idan ya yi takara da Mai girma Bola Tinubu
- Ministan ya bayyana cewa Amaechinko tikitin jam'iyyarsa ta ADC ba zai samu ba balle ya tsaya neman kuri'un 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan burin Rotimi Amaechi na yin takarar shugaban kasa da Bola Tinubu.
Nyesom Wike ya bayyana cewa Rotimi Amaechi, ba zai kai labari ba idan ya yi takara da Shugaba Tinubu a 2027.

Source: Facebook
Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv a ranar Talata, 19 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan
"Ka ajiye Shettima": An gayawa Tinubu wanda ya fi dacewa ya zama mataimakinsa a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan na birnin tarayya Abuja, ya ce ’yan Najeriya ba za su ba Amaechi dama a zaɓen 2027 ba.
Amaechi ya taba fafatawa da Tinubu
Rotimi Amaechi, wanda yanzu yake a jam’iyyar adawa ta ADC, ya zo na biyu a zaɓen fitar da gwani na shugaban kasa na APC a 2022, wanda tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, ya lashe.
A shekarar 2025, Amaechi ya fice daga APC ya koma ADC domin neman tikitin takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar a 2027.
Me Wike ya ce game da Amaechi?
Sai dai Wike, wanda shi ma tsohon gwamnan jihar Rivers ne kamar Amaechi, ya ce tsohon gwamnan ba zai samu tikitin ADC a 2027 ba.
"Shi (Amaechi) ya san ba zai samu tikitin ba. Na karanta inda ya ce ya san raunin shugaban kasa, don haka zai iya kayar da shi, amma ai ya riga ya san raunin shugaban kasa a 2022, lokacin da ya ba shi kashi a zaɓen fitar da gwani."

Kara karanta wannan
"Da bakinsu suka fada," Buba ya gano abin da Gwamnatin Tinubu ta shirya yi a zaben 2027
"Yan Najeriya sun san mutumin da za su ba tikiti, domin sun san wannan burin nasa (na Amaechi) ba zai kai labari ba."
- Nyesom Wike

Source: Facebook
Wike ya kuma soki Amaechi kan yaki da cin hanci da tabbatar da ingantaccen mulki, inda ya ce bai girmama kotu da bin doka ba a lokacin da yake gwamnan jihar Rivers.
Amaechi ya kasance gwamnan jihar Rivers daga watan Mayu 2007 zuwa Mayu 2015, lokacin da ya mika mulki ga Wike, wanda ya yi shekaru takwas a ofis.
Dangantaka tsakanin mutanen biyu ta yi tsami tun bayan nan.
An shawarci Tnubu ya ajiye Shettima
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar NENF ta yi kira da babbar murya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kujerar mataimakinsa, Kashim Shettima.
Kungiyar NENF ta bukaci Shugaba Tinubu, ya ajiye Kashim Shettima, domin ya dauko Kirista a matsayin wanda zai yi mataimaki a zaben shugaban kasa na 2027.
Ta nuna cewa tikitin Muslim-Muslim ya jawo Tinubu ya kasa samu kur'iu a wasu jihohin 'yankin Arewa ta Tsakiya, inda ta nuna yiwuwar tarihi ya sake maimaita kansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng