Adamawa: An Kama Matar da ke Sace Yara daga Arewa zuwa Kudu Ta Sayar da Su

Adamawa: An Kama Matar da ke Sace Yara daga Arewa zuwa Kudu Ta Sayar da Su

  • Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya mayar da yara 14 da aka sace hannun iyayensu bayan gano su a Anambra
  • An kama wata mata mai suna Ngozi Abdulwahab wadda ake zargi da safarar yaran daga Jambutu, Yola, zuwa Kudu
  • Gwamnatinsa ta yi alkawarin gurfanar da masu hannu a lamarin a gaban kotu tare da tallafa wa iyayen da aka sace musu ’ya’ya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa – Gwamnatin jihar Adamawa ta samu babbar nasara wajen yaƙi da safarar yara, bayan da aka ceto yara 14 da aka sace aka kai su Anambra domin sayar da su.

Yaran, waɗanda shekarunsu suke tsakanin hudu da tara, an mika su ga iyayensu a wajen bikin mika su da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Yola.

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

Lokacin da aka y bikin mika yaran da aka ceto ga iyayensu a Yola
Lokacin da aka yi bikin mika yaran da aka ceto ga iyayensu a Yola. Hoto: Adamawa State Government
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa mataimakiyar gwamna, Farfesa Kaletapwa Farauta, ce ta wakilci gwamna Ahmadu Fintiri, inda ta bayyana cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro ne ya kai ga wannan nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka gano yaran da aka sace

Bincike ya nuna cewa tun watan Yuli 2025 aka fara samun rahotannin ɓatan yara a sassan Adamawa, abin da ya sa jami’an tsaro suka sa ido sosai.

A cikin binciken ne aka gano cewa wata mata mai suna Ngozi Abdulwahab, ’yar asalin kabilar Igbo, ce ke jagorantar safarar yaran daga unguwar Jambutu a Yola ta Arewa.

Rahotonn TVC ya nuna cewa ana zargin tana jan yaran ne da ƙananan kayan ciye-ciye da kyaututtuka kafin ta tafi da su, ta boye su.

An bayyana cewa matar tana sayar da kowane yaro da aka ɗauko tsakanin ₦800,000 zuwa ₦1.7m, hakan ya tabbatar da yadda ta mayar da yara a matsayin kayan kasuwanci.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Boko Haram, Bakura ya karyata labarin kashe shi

An kama matar da ke satar yara

Mataimakiyar gwamna ta bayyana cewa an kama wadda ake zargi, yayin da bincike ke ci gaba domin gano duk wasu abokan aikinta.

Ta ce za a gurfanar da su bisa dokoki daban-daban ciki har da dokar kare yara ta Adamawa ta 2008.

A cewarta, wannan laifi “mummuna ne kuma mai tayar da hankali,” kuma gwamnati ba za ta yi sassauci ba wajen hukunta masu hannu a cikinsa.

Gwamna Fintiri ya aika da sakon gargadi

Gwamna Fintiri ya bayyana cewa jihar Adamawa za ta ci gaba da tsananta matakan tsaro domin hana masu safarar yara samun matsuguni.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su ƙara kula da ’ya’yansu, musamman waɗanda ba su kai shekaru 10 ba, ta hanyar kauce wa barin su tafiya makaranta ko kasuwa ba tare da rakiya ba.

Gwamna Ahmadu Fintiri yana hira da manema labarai a Yola
Gwamna Ahmadu Fintiri yana hira da manema labarai a Yola. Hoto: Adamawa State Government
Source: Facebook

Tallafin gwamnatin Adamawa ga iyalan yaran

Gwamnatin jihar ta bai wa kowane iyali da aka tsare musu ɗa tallafin kudi ₦100,000, tare da kayan abinci da na masarufi.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu

Farfesa Farauta ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da unguwanninsu, tare da kai rahoton duk wani abin da ke nuna alamun safarar yara ga jami’an tsaro cikin gaggawa.

Legit ta tattauna da Fatima Usman

Wata mata a jihar Adamawa mai suna Fatima Usman ta zantawa Legit cewa lallai an samu sace sacen yara a Yola da Mubi.

Fatima ta ce:

"Muna rokon Allah ya kare mu da yaran mu. Amma abin babu dadin ji gaskiya."

An kama makamai ana shirin safararsu

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun kama wata mota dauke da tarin makamai ana shirin tafiya da su jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa motar ta fito ne daga Maiduguri na jihar Borno kuma ana zargin wani soja da hannu a lamarin.

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an kama motar ne a karamar hukumar Nafada da ke iyakar Gombe da Yobe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng