Gwamnan Borno, Babagana Zulum Zai bar APC, Ya Shiga Hadakarsu Atiku? An Ji Gaskiya

Gwamnan Borno, Babagana Zulum Zai bar APC, Ya Shiga Hadakarsu Atiku? An Ji Gaskiya

  • Gwamna Babagana Zulum ya musanta jita-jitar da ake yadawa na cewa zai sauya sheka zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar
  • Farfesa Zulum ya tabbatar da cewa biyayyarsa ga APC na nan daram, yana mai jaddada kwazonsa ga ci gaban al'ummar Borno
  • Ya roƙi jama'a da su yi watsi da ire-iren waɗannan rahotanni, yayin da ya nemi 'yan jarida su riƙa tantance bayanai kafin yaɗawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa zai fice daga APC zuwa jam’iyyar adawa ta ADC tare da wasu gwamnoni biyar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya bayyana rahoton a matsayin tsantsagwaron ƙarya da wasu ke yaɗawa domin cimma wata manufa ta siyasa.

Gwamna Babagana Zulum ya nesanta kansa daga jita-jitar sauya sheka zuwa ADC
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce har yanzu yana nan APC daram. Hoto: @ProfZulum
Asali: Twitter

Martanin Zulum kan jita-jitar barin APC

Channels TV ta rahoto Gwamna Babagana Zuluma yana sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC, yana mai cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun samu labarin wani rahoton ƙarya da ya fara yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke da'awar cewa ni da wasu gwamnoni biyar za mu fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.
“Wannan jita-jita ba ta da wani tushe, kuma wasu masu son bata mana suna ne suke yayata wannan ƙirƙirarren labarin.
"Wadanda ke yaɗa irin wannan labari ba su da wata gudunmawa ga ci gaban jihar Borno ko Najeriya gaba ɗaya. Wannan shi ne abin da za a kira ƙage da 'yan adawa suka saba yi."

"Za mu ci gaba da mulki a APC" - Zulum

Gwamna Zulum ya kara da cewa:

“Biyayyata ga jam’iyyar APC tabbatacciya ce, kuma nakan sadaukar da kaina ne domin jin daɗi da ci gaban jihar Borno.”

Ya kuma bukaci jama’ar jihar Borno da sauran ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan jita-jita, a cewar rahoton Punch.

Gwamna Babagana Zulum ya ce zai ci gaba da yiwa jihar Borno hidima a karkashin APC
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce har yanzu yana nan APC daram. Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

A cewarsa, gwamnatin jihar Borno ba ta da lokacin yin siyasar banza saboda “a halin yanzu muna da ayyuka masu yawa na sake ginawa da bunƙasa jiharmu.”

Ya kuma shawarci kafafen yaɗa labarai da jama’a da su rika tantance sahihancin labarai daga majiyoyin da suka dace, su kuma guji yaɗa ƙarya daga masu neman suna ko ɓata-gari.

“Zamu ci gaba da gudanar da mulkin jihar Borno a ƙarƙashin tutar jam’iyyarmu mai girma ta APC,” in ji sanarwar.

Su Atikun sun kaddamar da jam'iyyar ADC

Tun da fari, mun ruwaito cewa haɗakar shugabannin adawa sun zabi ADC a matsayin jam'iyyar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Wadanda suka assasa wannan kawance sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi.

Sauran sun hada da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai; da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, wanda aka naɗa a matsayin sakataren rikon kwarya na jam’iyyar ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.