Duniya Labari: An Yi Babban Rashi, Shugaban Ƙaramar Hukuma a Jigawa Ya Rasu
- Shugaban karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa, Hon. Lawan Ya’u, ya rasu da yammacin Asabar, 5 ga Yuli, yana da shekara 61.
- Ya rasu ne a wani asibitin kudi da ke Kano bayan gajeriyar rashin lafiya, inda aka ce ciwon zuciya ne ya kama shi
- Ya bar mata biyu da 'ya'ya da dama, za a yi jana'izarsa safiyar Lahadi a Gumel, marigayin ya fara aiki tun 2024 a matsayin shugaban karamar hukuma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - An yi babban rashi a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya bayan rasuwar shugaban karamar hukuma.
An sanar da rasuwar shugaban karamar hukumar Gumel da ke jihar, Hon. Lawan Ya’u a yau Asabar 5 ga watan Yulin 2025.

Asali: Original
Shugaban karamar hukuma a Jigawa ya rasu
Rahoton Leadership ya tabbatar da samun labarin rasuwar marigayin ta bakin wani dan uwansa a yau Asabar 5 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce marigayin ya rasu da yammacin yau Asabar, 5 ga watan Yuli, 2025 yana da shekara 61 a wani asibiti da ke Kano.
Hon. Ya’u ya rasu ne a wani asibitin kudi da ke jihar Kano bayan gajeriyar rashin lafiya da ya kamu da ita a cikin kwanaki kalilan.
Wani dan uwa daga cikin iyalansa ya bayyana cewa:
"An garzaya da mamacin asibiti tun ranar Juma’a sakamakon zargin kamuwa da ciwon zuciya.
“Abin takaici, ya rasu da yammacin Asabar yayin da yake samun kulawa daga likitoci a asibitin da aka kwantar da shi."

Asali: Facebook
Yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomi
Majiyoyi sun ruwaito cewa kafin zabensa a matsayin shugaban karamar hukumar Gumel a watan Agustan 2024, ya kasance tsohon ma'aikacin gwamnati a jihar.
Jam’iyyar APGA da AP sun lashe kujerun kansiloli a zaɓen kananan hukumomi da aka gudanar a jihar Jigawa.
Sai dai jam’iyya mai mulki ta APC ce ta yi nasara gaba ɗaya, inda ta lashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 27.
Har ila yau, APC ta kuma kujeru lashe kujerau 281 daga cikin 287 na kansiloli a zaɓen da jam’iyyu 11 suka fafata.
Yaushe za a gudanar da jana'izar marigayin?
An tabbatar da cewa marigayin ya mutu ya bar iyalai da dama wadanda suka hada da mata biyu da ‘ya’ya da yawa.
Har ila yau, an ce za a gudanar da sallar jana’izarsa da safiyar Lahadi 6 ga watan Yulin 2925 a cikin tsohuwar birnin Gumel da ke jihar Jigawa.
Majalisa ta yi jimamin rashin mambanta daga Jigawa
Kun ji cewa majalisar wakilan tarayya ta yi alhinin rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta daga jihar Jigawa, Honorabul Isa Dogonyaro.
Dogonyaro ya riga mu gidan gaskiya ne ranar Jumu'a bayan fama da gajeriyar rashin lafiya,ya rasu yana da shekaru 46 a duniya.
A wata sanarwa, majalisar ta yi ta'aziyya da addu'o'i ga marigayin tare da fatan Allah ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa.
Asali: Legit.ng