Jigawa: Tsautsayi Ta Rutsa da Bafaden Sarki a Kokarin Hana Hawan Doki, Ya Mutu a Asibiti

Jigawa: Tsautsayi Ta Rutsa da Bafaden Sarki a Kokarin Hana Hawan Doki, Ya Mutu a Asibiti

  • Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar wani mai gadin fada bayan wani gangamin dawakai ba bisa ka’ida ba a Gumel, jihar Jigawa
  • An ce wasu matasa daga Gumel, ciki har da Ibrahim Gwani da Goni, sun shirya gangamin dawakai ba tare da izini ba, wanda ya janyo tashin hankali
  • Gadar Abdulhadi Mana ya rasa ransa bayan dawakai suka buge shi yayin da ya je tarwatsa gangamin. Ana ci gaba da bincike da neman wadanda suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gumel, Jigawa - Masarautar Gumel a jihar Jigawa ta yi rashin daya daga cikin fadawanta bayan an samu hatsaniya dalilin hawa dawaki.

Rahotanni sun ce wasu matasa ne suka shirya bikin ba tare da izinin hukumomi ba wanda a karshe ya koma rigima.

An yi rashin bafaden Sarki a Jigawa
Wani bafaden Sarki ya rasa ransa a Jigawa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda bafaden Sarkin Gumel ya rasu

Majiyoyin Zagazola Makama ta ce lamarin ya faru ne a ranar 24 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 5:30 na yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani bafade bayan wani gangamin hawa dawaki ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Gumel.

An ce wasu matasa ne waɗanda yanzu haka sun tsere suka shirya gangamin dawakai ba tare da izini ba a yankin.

Daga cikinsu an ce akwai Ibrahim Gwani da Goni daga Gumel, tare da wasu matasa da ba a bayyana sunansu ba.

An ruwaito cewa gangamin da bai samu izini ba ya haddasa firgici a yankin, lamarin da ya sa fadar Sarki sarki ta turo masu gadi domin tarwatsa su.

“Abin takaici, daya daga cikin masu gadi, Abdulhadi Mana, ya fadi sakamakon bugewar dawakai yayin da ake kokarin dawo da doka.
"An garzaya da shi asibitin Gumel, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa."

Cewar ‘yan sanda.

‘Yan sandan sun kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike tare da kokarin cafke wadanda suka tsere da ke da hannu a lamarin.

Rundunar ta gargadi jama’a da kada su shirya taron jama’a ba tare da samun izini ba domin kaucewa tayar da hankula da barazanar tsaro.

Fadar Gumel ta yi jimamin mutuwar bafadenta
Doki ya buge bafaden Sarkin Gumel. Hoto: Fadar Gumel.
Asali: Facebook

Fadar Gumel ta yi jimamin mutuwar bafadenta

Fadar Gumel ya fitar da sanarwa a shafin Facebook inda take alhinin rashin jajirtacce da aka yi a birnin.

Birnin Gumel na cikin jimamin rashin wani haziki, Abdulhadi Kauran Dogoran Gumel.

Marigayin ya rasa ransa bayan da doki ya buge shi yayin da yake ƙoƙarin dakatar da wasu mahaya a lokacin Sukuwar Dawakai.

Ta ce wannan mummunan lamari ya faru ne lokacin da Abdulhadi, wanda aka san da jajircewa, ya shiga tsakani domin ya ja kunnen mahayan don hana tarzoma a cikin gari.

Masarautar ta ce mutuwar Abdulhadi ta bar babban gibi a zukatan jama’a, inda kowa ke alhini da addu’ar Allah ya jikansa da rahama.

Masarautar Gumel ta sa doka kan kayan aure

Kun ji cewa Masarautar Gumel ta kafa sabbin dokokin kayyade kayan aure a yankinta domin saukakawa matasa aure.

Masarautar ta dauki wannan mataki ne sakamakon halin da al'umma ke fama da shi da matsin tattalin arziki.

A wata takardar mai dauke da sa hannun Sakataren Masarautar kuma Maji Dadin Gumel, an umurci limaman Juma'ar Masarautar su fadakar da al'umma kan wannan sabuwar doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.