Majalisa Ta Yi Jimami da Ɗan Majalisar Tarayya, Dogonyaro Ya Rasu a Abuja

Majalisa Ta Yi Jimami da Ɗan Majalisar Tarayya, Dogonyaro Ya Rasu a Abuja

  • Majalisar wakilan tarayya ta yi alhinin rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta daga jihar Jigawa, Honorabul Isa Dogonyaro
  • Dogonyaro ya riga mu gidan gaskiya ne ranar Jumu'a bayan fama da gajeriyar rashin lafiya,ya rasu yana da shekaru 46 a duniya
  • A wata sanarwa, majalisar ta yi ta'aziyya da addu'o'i ga marigayin tare da fatan Allah ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dokoki ta ƙasa ta aike da saƙon ta'aziyyar ɗaya daga cikin mambobinta, Isa Dogonyaro, mai wakiltar mazaɓar Babura/Garki a jihar Jigawa.

Ɗan majalisar tarayya, Isa Dogonyaro ya rasu ne ranar Jumu'a, 10 ga watan Mayu a birnin tarayya Abuja bayan fama da gajeriyar rashin lafya.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC, ta hana su aikin majalisa

Majalisa ta yi alhinin rashin Isa Dogonyaro.
Majalisar wakilan tarayya ta jajantawa iyalan ɗan majalisar Garki/Babura Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Mai magana da yawun majalisar wakilai ta ƙasa kuma shugaban kwamitin midiya da yaɗa labarai, Akin Rotimi Jr, ne ya miƙa sakon ta'aziyyar a wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana rasuwar Dogonyaro a matsayin babban rashi ga majalisar da ma Najeriya baki ɗaya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Dogonyaro mutum ne mai ƙwazo" - Majalisa

Sanarwan ta ce:

"Cikin jimami muke sanar da rasuwar Isa Dogonyaro (Kogunan Ringim), dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Babura/Garki ta jihar Jigawa a majalisar wakilai ta 10.
"Marigayi Honorabul Isa Dogonyaro ya kasance dan majalisa mai kwazo kuma mai kishin kasa wanda ya yi wa al’ummar mazabarsa da kasa baki ɗaya hidima.
"Ya kasance ginshiki a majalisa, ya bayar da gudunmawa sosai wajen samar da dokoki, musamman a fannin yaki da cutar kanjamau, tarin fuka, da yaki da zazzabin cizon sauro, inda ya rike mukamin mataimakin shugaban kwamiti."

Kara karanta wannan

Bayan Rahama Sadau, wata jarumar fina finai ta sake samun mukami a Abuja

Majalisa ta aika saƙon ta'aziyyar Doganyaro

Kakakin majalisar ya ƙara da addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma bai wa iyalansa, mutanen mazaɓa da al'ummar jihar Jigawa haƙurin jure rashin.

A rahoton Leadership, Rotimi Jr ya ci gaba da cewa:

“A wannan lokaci na jimami, addu’o’inmu suna tare da iyalansa, mazabarsa, abokan aikinsa, da al’ummar Jihar Jigawa. Muna addu'ar samun juriya da ta'aziyya ga duk waɗanda wannan rasuwa ta shafa."

Gwamna Ododo ya bada tabbacin ceto ɗalibai

A wani rahoton Gwamna Ahmed Ododo ya tabbatar wa iyaye da al'ummar jihar Kogi cewa za a ceto ɗaliban jami'a da aka sace cikin ƙoshin lafiya.

Ododo ya bayyana cewa yanzu haka jami'an tsaro da ɗaruruwan mafarauta da suka san yankin sun bazama domin ceto ɗaliban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel