ADC: Haɗakar Atiku Ta Fara Karfi, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Fice daga PDP

ADC: Haɗakar Atiku Ta Fara Karfi, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Fice daga PDP

  • Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark ya fice daga PDP tare da komawa jam'iyyar haɗakar ƴan adawa watau ADC
  • David Mark ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda rigingimun cikin gida da suka addabi PDP, waɗanda aka gaza shawo kansu
  • Wannan dai na zuwa sa'o'i kaɗan bayan haɗakar adawa ta amince da naɗin Mark a matsayin shugaban ADC na rikon ƙwarya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP.

David Mark ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa da makusantansa na siyasa duba da halin da PDP ta tsinci kanta a ciki.

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.
Sanata David Mark ya miƙa takardar barin PDP a jihar Benue Hoto: @SenDavidMark
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne wata wasiƙa ta murabus da tsohon sanatan ya rubuta wacce jaridar Daily Trust ta gani ranar Laraba, 2 ga watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan siyasar, wanda ya fito daga jihar Benue ya bayyana cewa rikicin shugabancin PDP ta har yanzu aka gaza warware shi ne ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar.

David Mark zai jagoranci jam'iyyar haɗaka, ADC

A daren Talata, haɗakar ƴan adawa ta amince da David Mark tare da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugabannin ADC na riƙo.

Hakan ya biyo bayan amincewa da ADC da jagororin adawa suka yi a matsayin jam'iyyar da za su tunkari zaɓen 2027 domin kawar da APC.

A cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaban PDP na mazabarsa da ke Otukpo, Jihar Benue, David Mark ya ce matsalolin cikin gida da suka addabi jam'iyyar sun sa ta zama abin kunya a idon jama'a.

Tsohon shugaban Majalisar dattawa ya bar PDP

“Ina miko gaisuwa tare da girmamawa ga ‘yan PDP a mazabar Otukpo 1, jihar Benue da Najeriya baki ɗaya. Na rubuto wannan wasiƙa ne domin sanar da ku hukuncin da na yanke na ficewa daga PDP.

“Kamar yadda kuka sani, na shafe tsawon shekaru a PDP kuma na nuna ƙwazo da sadaukarwa ga akidunta.
"Duk da yadda mafi yawan ‘yan jam’iyya suka fice bayan faduwar zaɓen shugaban ƙasa na 2015, na sha alwashin ci gaba da zama a PDP ko da kuwa ni kaɗai na rage."

- David Mark.

Mukaddashin shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum.
David Mark ya ce PDP ya zama abin kunya a wurin ƴan Najeriya Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

David Mark ya rungumi haɗakar ƴan adawa

Ya ce duk wani ƙoƙari da aka yi na sulhu da gyara jam’iyyar PDP domin dawo da martabarta ya ci tura, kuma abubuwan da suka faru kwanan nan sun ƙara ƙassara ta sosai.

A rahoton Channels tv, David Mark ya ƙara da cewa:

“Bayan shawarwari da iyalina, abokaina, da abokan siyasa, na yanke shawarar shiga cikin sabuwar haɗakar ƴan adawa, a wani ɓangare na ƙoƙarin ceto ƙasarmu da kare dimokuraɗiyyar da muka yi wahalar samu.”

Haɗakar Atiku ta zaɓi jam'iyyar siyasa

A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyar hadakar 'yan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta ta zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta kalubalantar APC a 2027.

Wannan mataki ya biyo bayan ganawar da shugabannin ƙungiyar suka gudanar tun daga ranar Talata har zuwa wayewar garin yau Laraba a Abuja.

Haɗakar dai ta lashi takobin yin duk mai yiwuwa wajen karɓe ragamar shugabancin Najeriya daga hannin APC a babban zaɓe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262