2027: Rikicin Shugabanci Ya Barke a ADC bayan Kulla Hadakar 'Yan Adawa
- Wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC sun fito karara sun ƙi amincewa da nadin Rauf Aregbesola a matsayin sakatare na rikon kwarya
- Rahotanni sun nuna cewa sun ce ba a bi ka’ida ba wajen nadin, kuma an ƙi tuntubar shugabanni a matakin jihohi da ƙasa
- Sun gargadi masu ƙoƙarin 'sayar' da jam’iyyar cewa ADC mallakin mambobinta ce, ba ‘yan siyasa masu 'saye da sayarwa ba'
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, FCT – Wata sabuwar rigima ta ɓarke a cikin jam’iyyar ADC, bayan nadin tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakataren rikon kwarya na jam’iyyar.
Wasu mambobi da shugabannin jam’iyyar karkashin jagorancin mai magana da yawun jam’iyyar, Dr. Musa Isa Matara, sun fito fili sun soki matakin.

Source: Twitter
Jaridar the Guardian ta ce sun soki matakin ne suna masu cewa nadin ba bisa ka’ida ba ne kuma wata hanya ce ta mamaye jam’iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bayyana cewa ADC ba ta sayarwa ba ce, kuma ba za su amince da wani yunƙuri na tilasta haɗin gwiwa da wasu 'yan adawa ba tare da tuntubar membobin jam’iyyar ba.
Shugabannin ADC sun yi korafi kan hadaka
Dr Matara ya bayyana cewa har yanzu ba a yi wani taron gangamin jam’iyyar ko na kwamitin zartaswa (NEC) da zai sahale wannan sauyi na shugabanci ba.
A cewarsa:
“Ba mu da matsala da haɗin gwiwa ko sauye-sauyen gyara, amma muna da matsala da mamaye jam’iyya, da naɗe-naɗen da ba su da tushe,'
Matara da tawagarsa sun ce babu wata doka ko alfarma da ke bai wa Aregbesola damar zama wakilin jam’iyya a matakin ƙasa ba tare da amincewar mambobi ba.
'Yan ADC sun ce ba a cimma hadaka ba
'Yan jam'iyyar sun ƙaryata ikirarin da ke cewa ADC ce dandalin sabuwar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa da ke neman kayar da APC a 2027.

Kara karanta wannan
Jama'atul Nasril Islam ta yi magana kan karuwar kashe kashe da farfadowar Boko Haram
A cewar 'yan jam'iyyar:
“Ya zama dole a tabbatar da cewa yawancin mambobin jam’iyyar ba su da masaniya a kan wannan haɗin gwiwa da ake ta yayatawa.
"Idan wani na ƙoƙarin tilasta haɗin kai ba tare da amincewar tushe ba, to wannan cin zarafin dimokuraɗiyya ne,”

Source: Twitter
'Yan jam'iyyar ADC sun gargadi 'yan adawa
'Yan jam'iyyar sun gargaɗi waɗanda ke ƙoƙarin shigo da ADC cikin haɗin gwiwar adawa da su yi hattara, domin wasu mutane ne ke yunƙurin sayar da ruhin jam’iyyar don amfaninsu.
“ADC ba kasuwa ba ce, kuma ba kayan sayarwa ba ce. Jam’iyyar mallakin mambobinta ce – ba ta ‘yan siyasa da ke da wata manufa ba ce”
- Inji su.
Martanin APC kan hadakar 'yan adawa a ADC
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta ce ba ta da wata damuwa kan hadakar da 'yan adawa suka yi.
Mai magana da yawun APC, Bala Ibrahim ya ce jam'iyyarsu ta riga ta kafu kuma tana da goyon bayan jama'a.
Bala Ibrahim ya yi martani wa tsohon gwamnan jihar Jigawa da tsohon shugaban majalisar dattawa kan sukar Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
