INEC za Ta Gudanar da Zaɓen Cike Gurbi a Kano da Jihohi 11, An ba Jam'iyyu Umarni
- INEC ta shirya zaɓen cike gurbi a jihohi 12 a ranar 16 ga Agusta, 2025, don cike gurbin kujeru 16 na majalisar tarayya da jihohi
- Farfesa Mahmood Yakubu ya ce babu kowa a kan kujerun da za a cike gurbin su ne saboda murabus, mutuwa ko kuwa soke zaɓe
- Sai dai INEC ta ce an dage zaɓen cike gurbi a mazabu biyu na jihohin Rivers da Zamfara saboda dokar ta-baci da shari'ar da ake yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta sanya ranar da za ta gudanar da zaɓukan cike gurbi sassan Najeriya.
INEC ta ce za ta gudanar da zaɓukan a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, domin cike gurbin kujerun ƴan majalisun tarayya da na jihohi a faɗin jihohi 12 na ƙasar.

Asali: Getty Images
INEC za ta gudanar da zaɓen cike gurbi
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da hakan ne yayin wani taro da ya yi da shugabannin jam'iyyun siyasa a Abuja ranar Alhamis, a cewar sanarwar shafin hukumar na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa kujerun da za a cike sun kasance babu kowa a kansu sakamakon murabus, mutuwa, da kuma umarnin kotu na soke zaɓe.
"Waɗannan zaɓukan za su gudana a mazabu 16 da suka haɗa da kujeru biyu na majalisar dattawa, kujeru biyar na majalisar wakilai, da kujeru tara na majalisar jiha," a cewar Farfesa Yakubu.
Mazabun da za a gudanar da zaɓe a jihohi 12
Mazabun da abin ya shafa sun haɗa da mazabar sanata ta Anambra ta Kudu da Edo ta Tsakiya; da kuma mazabar majalisar wakilai ta Ovia ta Kudu maso Yamma/Ovia ta Kudu maso Gabas da ke a jihar Edo.
Sauran kujerun ƴan majalisar wakilai da za a sake wa zaɓen su ne: Babura/Garki (Jigawa), Chikun/Kajuru (Kaduna), Ikenne/Shagamu/Remo ta Arewa (Ogun), da Ibadan ta Arewa (Oyo).
Kujeru tara na majalisar jiha da za a gudanar da zaben cike gurbin sun haɗa da: Ganye (Adamawa), Onitsha ta Arewa I (Anambra), da Dekina/Okura (Kogi).
Sauran su ne: Zaria Kewaye da Basawa (Kaduna), Bagwai/Shanono (Kano), Mariga (Neja), Karim Lamido I (Taraba), da Kauran Namoda ta Kudu (Zamfara).
Farfesa Yakubu ya ce hukumar za ta tura jami'ai 30,451 don gudanar da zaɓukan, waɗanda za su shafi masu jefa ƙuri'a 3,553,659 da suka yi rajista a faɗin kananan hukumomi 32, gundumoni 356, da kuma rumfunan zaɓe 6,987.
Wasu mazabu da aka ɗage zaɓen cike gurbinsu
Sai dai, INEC ta tabbatar da cewa ba za a gudanar da zaɓen cike gurbi a mazabu biyu na majalisar jiha ba a halin yanzu.

Asali: Twitter
Mazabar farko ita ce Khana II a jihar Rivers, saboda dokar ta-baci da ke aiki a yankin; sai kuma Talata Mafara ta Kudu jihar Zamfara, wacce ake kan tafka shari'a game da ita.
Bugu da ƙari, Farfesa Yakubu ya sanar cewa za a sake gudanar da zaɓuka a wasu mazaɓu, bisa umarnin da kotu ta bayar.
Inda za a gudanar da zaben su ne: Enugu ta Kudu I (Enugu) da Ghari/Tsanyawa (Kano), kuma za a yi zaben a ranar 16 ga Agusta. An taɓa samun tashin hankali a waɗannan zaɓukan na baya.
Yaƙin neman zaɓe da rajistar masu kaɗa ƙuri'a
Rahoton ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaɓen fitar da gwani tsakanin 17 zuwa 21 ga watan Yuli, 2025.
Za a miƙa fom ɗin takara ta yanar gizo daga 22 zuwa 26 ga Yuli, yayin da za a fara ayyukan yaƙin neman zaɓe daga ranar 2 ga Agusta har zuwa daren ranar 14 ga Agusta.
Farfesa Yakubu ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da aikin yiwa masu jefa kuri'a rajistar, domin karbar katin zaɓe na dindindin a duk faɗin ƙasar.
Karanta sanarwar INEC a nan ƙasa:
Shugabanni da jiga-jigan PDP sun gana da INEC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, PDP ta kai ziyara hedikwatar INEC domin warware ruɗanin da ya taso kan taron kwamitin NEC na jam’iyyar.
Muƙaddashin shugaban PDP, Umar Damagum, ya ce sun je INEC ne domin warware rikicin shugabancin jam’iyyar da ke haifar da ruɗani.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce PDP na yawan kawo ruɗani game da matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng