Shugabanni da Jiga Jigan PDP Sun Gana da INEC a Abuja, An Ji Abin da Suka Tattauna

Shugabanni da Jiga Jigan PDP Sun Gana da INEC a Abuja, An Ji Abin da Suka Tattauna

  • Tawagar PDP ta kai ziyara hedikwatar hukumar zabe ta kasa watau INEC domin warware ruɗanin da aka samu game da taron NEC
  • Muƙaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum ya ce sun ziyarci INEC ne domin warware ruɗanin shugabancin jam'iyyar
  • Shugaban INEC, Mahmud Yakubu ya ce PDP tana yi wa hukumar yawo da hankali game da kujerar sakataren jam'iyyar na ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugabannin PDP da manyan jiga-jigai ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagum, sun kai ziyara hedkwatar INEC.

Wannan babbar tawaga ta kai ziyara hedkwatar hukumar zaɓe ta ƙasa watau INEC ne domin warware rikicin shugabancin PDP, wanda ke ci gaba da haifar da ruɗani.

Tawagar PDP ta ziyarci INEC a Abuja.
Shugabannin PDP sun gana da wakilan INEC kan taron NEC Hoto: @INECNigeria
Asali: Twitter

INEC ta tabbatar da karɓar baƙuncin tawagar PDP a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X ranar Talata, 24 ga watan Yuni, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin ziyarar, tawagar PDP ta gana da wakilan INEC ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu.

Gwamnoni da ƙusoshin PDP da suka je INEC

Tawagar ta ƙunshi manyan jiga-jigan PDP da suka haɗa da: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki; gwamnoni, Bala Mohammed (Bauchi), Seyi Makinde (Oyo), Dauda Lawal (Zamfara) da Caleb Mutfwang (Filato)

Sai kuma tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da, Sanata Ahmed Makarfi (Kaduna) Sanata Seriake Dickson (Bayelsa); da kuma Sanata Ben Obi da wasu jiga-jigai.

Yayin ganawa da jami’an INEC, Damagum ya ce sun kawo wannan ziyara ne domin tattaunawa kan wasiƙar da hukumar ta aike wa PDP game taron kwamitin zartarwa (NEC).

Damagum ya ce bayan hukuncin kotun koli, ya zama wajibi PDP ta sanar da INEC ci gaban da aka samu game da kujerar sakatarenta na ƙasa.

Shugaban INEC ta faɗi dalilin shirya taron

Da yake mayar da martani, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta kira wannan taron ne bisa buƙatar jam'iyyar PDP.

Ya jaddada cewa INEC na buƙatar sanin su waye sahihan shugabannin jam'iyyar, musamman saboda ruɗanin da aka samu kan takardar gayyatar taron NEC na PDP.

"A duk tarukan NEC 99 da PDP ta gudanar a baya, INEC na karɓar wasiƙun gayyata ɗauke da sa hannun shugaban jam’iyya da kuma sakatare.
“Amma a wannan karon, wasiƙar na ɗauke da sa hannun shugaban jam’iyyar PDP ne kaɗai, hakan ya sa muke buƙatar ƙarin bayani.”

Rikicin PDP kan kujerar sakataren jam'iyya na ƙasa

Dangane da batun sakataren PDP na ƙasa, shugaban INEC ya ce:

“Kwanakin baya, INEC ta karɓi wasiƙa daga PDP da ke nuna cewa Ude Okoye ne sakataren jam’iyya. Daga baya kuma sai aka aiko da wata wasiƙar da ke cewa Sanata Anyanwu ne.
Sannan daga baya sai aka ce Shokoya ne, daga bisani kuma sai jam’iyyar ta sake cewa Sanata Anyanwu ne. A wannan taron muke son gane inda aka kwana.

Gwamna Lawal ya faɗi tushen rikicin PDP

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya ce ba Atiku Abubakar ne kaɗai ya jawo rigingimu a cikin jam'iyyar PDP ba.

Gwamna Dauda Lawal ya ce asalin rikicin PDP ya fara ne daga girman kai na wasu tsirarun ƴaƴan jam'iyyar, wanda ya yaɗu har yake neman fin karfinta.

Gwamnan na jihar Zamfara ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa za a warware rikicin domin suna ƙoƙarin ganin an cimma hakan nan ba da jimawa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262