Bayan Masu Shirin Haɗaka Sun Zaɓi ADA, an Fadi Gwamnonin PDP 2 da Za Su Koma APC
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Gwamna Siminalayi Fubara da Douye Diri su ne na gaba da za su koma APC
- Akpabio ya bayyana hakan a wani taron maraba da Umo Eno na Akwa Ibom zuwa jam’iyyar APC, inda manyan jiga-jigan jam’iyyar suka halarta
- Ya ce yankin Kudu maso Kudu zai kada kuri’a sosai a 2027 domin Bola Tinubu, yana ganin “za a samu kashi 99.9 cikin dari"
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana yadda wasu gwamnoni suka shirya dawowa APC.
Akpabio ya ce Siminalayi Fubara wanda aka dakatar daga mukamin gwamnan Rivers da Douye Diri na Bayelsa, za su koma APC.

Asali: Facebook
An yi taron karbar gwamna zuwa APC
Akpabio ya bayyana haka ne ranar Asabar yayin taron maraba da Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom zuwa jam’iyyar mai mulki ta APC, TheCable .
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da taron ne a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje da wasu gwamnoni da sanatoci sun halarci taron.
A ranar 6 ga Yunin 2025 da muke ciki, Gwamna Eno ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Akpabio ya ce taron ba sauya sheka kawai ba ne, amma wani shiri ne da “komawar Akwa Ibom cikin Najeriya.”

Asali: Facebook
Akpabio ya fadi karfin APC a Kudu maso Kudu
Shugaban majalisar dattawan, wanda tsohon gwamna ne, ya ce sauya shekar Eno da Sheriff Oborevwori na nuni da sauyin siyasa a Kudu maso Kudu.
Ya ce:
“Yau, Gwamna Otu ba gwamna kadai ba ne. Mun gode da tarbar ’yan’uwa. Za a tarbi karin ’yan’uwa nan gaba.
“Gwamna Sheriff na Delta, mun gode da shigowa jam’iyyar masu kawo cigaba da tafiyar da Kudu maso Kudu gaba.
“Gwamna Uno Eno, bayan ka, wa ya sani? Jihar Rivers za ta sauya. Bayan Rivers, Bayelsa za ta biyo.
Alƙawarin Akpabio ga Tinubu a zaɓen 2027
Akpabio ya kara da cewa yankin Kudu maso Kudu zai kada kuri’a sosai domin nasarar Bola Tinubu a zaben 2027.
“Zuwa 2027, Kudu maso Kudu zai kada kuri’a daya. Kudu maso Kudu zai zabi Bola Tinubu a 2027.
“Ina ganin za ka zama gwamna na farko da aka sake zaba a 2027. Shugaban kasa zai samu kashi 99.9 cikin dari.”
- Cewar Akpabio
A yanzu haka, jam’iyyar APC na rike da jihohi hudu daga cikin shida a yankin Kudu maso Kudu. Rivers da Bayelsa ne kadai ba APC ba.
El-Rufai, Atiku sun zabi jam'iyyar haɗaka
Kun ji cewa, haɗakar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ke jagoranta ta amince da ƙirƙiro sabuwar jam'iyyar siyasa.
Atiku da sauran yan adawa sun buƙaci yi wa jam'iyyar ADA rijista bisa tsarin doka ga hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi na cikin manyan ƴan siyasa da ke jagorantar haɗakar.
Asali: Legit.ng