Sheikh Jingir Ya Magantu kan Rigimar Raba Tinubu da Kashim Shettima kafin Zaɓen 2027

Sheikh Jingir Ya Magantu kan Rigimar Raba Tinubu da Kashim Shettima kafin Zaɓen 2027

  • Muhammad Sani Yahaya Jingir ya magantu kan munafukai na kokarin raba Bola Tinubu da Kashim Shettima kafin zaben 2027 mai zuwa
  • Malamin ya ce Muslim/Muslim ya hada Bola Tinubu da Shettima ne baki daya, ba wai a ware daya daga cikin su ba kamar yadda wasu ke kokarin yi
  • Jagoran na Izala a Jos, Sheikh Jingir ya ce ba duk Musulmi yake nufi ba, sai nagari, inda ya roki Allah SWT ya tarwatsa masu kokarin raba su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Shugaba a kungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya yi magana kan zaben Muslim/Muslim a shekarar 2027.

Wannan martani na shehin malamin bai rasa nasaba da rigimar neman sauya Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Jingir ya magantu kan zaben Tinubu da Kashim Shettima
Sheikh Jingir ya soki masu neman raba Tinubu da Shettima. Hoto: Sheikh Sani Yahaya Jingir, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Jingir ya kare mulkin Tinubu da Shettima

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Halifa Shuaibu Akwana ya wallafa a shafin Facebook a jiya Laraba Alhamis 18 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Sheikh Sani Jingir ya ce akwai munafukai da ke nufin farraka Bola Tinubu da Kashim Shettima kafin zaɓen 2027.

Ya ce lokacin da suka bukaci a zabi Muslim Muslim ba su ce a zabi Tinubu shi kadai ba.

A cewarsa:

"Muka ce zamu zabi Muslim/Muslim, akwai maganar zaben Tinubu a ciki ko babu?
"Da muka ce Muslim/Muslim akwai batun Kashim Shettima a ciki ko babu? Don Allah mun zabe su a hade ko kuma a rabe?
"Allah ya kare Ahmad Bola Tinubu, Allah ya kare Kashim Shettima, Allah ya kare masu goyon bayan gaskiya a gwamnatinsu.
"Allah ya kare wadannan bayin Allan daga sharrin munafukai, idan Allah ya yarda gwamnatin Muslim/Muslim za ta sake yin nasara.
Jingir ya kare takarar Tinubu da Shettima
Sheikh Jingir ya goyi bayan takarar Tinubu da Shettima a 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Tinubu-Shettima: Jingir ya yi addu'o'i ga munafukai

Sheikh Jingir ya roƙi Allah ya tarwatsa duk mai son kawo sabani a tsakanin Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Ya ce suna magana ne kan Musulmi nagari ba lalatacce da ke sallah da shan giya ko cin amana da yin zina ba.

Ya ce:

"Waɗanda za su tsaya akwai Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, Allah duk shedanin da yake son raba su ka kawar da shi.
"Allah ka taimaki wadannan bayi naka, ka rushe masu neman raba kansu, ni fa idan ka ji na ce Muslim Muslim ba ina nufin rubabben Musulmi ba ga sallah ga shan giya.
"Ko kuma ga sallah ga cinye bashi, ga sallah ga zina ba da su nake ba idan ka ji na yi magana da mai kyan na ke fada."

Wani mabiyin Malam ya tattauna da Legit Hausa

Umar Ibrahim Adam ya ce tabbas suna tare da Malam a bangarori da dama na addini amma ba a siyasa ba.

Ya ce:

"Malam shugaba ne kuma ina mutunta shi fiye da kima amma muna da bambancin ra'ayi na siyasa.
"Hakan ba shi ke nuna babu mutuntawa ba, kowa yana da zabinsa a zuciya kuma ina mutunta layin da ya kama."

Umar ya shawarci al'umma su yi addu'ar neman shugabanni masu alheri fiye da wadanda suke so.

Jingir ya kare Tinubu kan farashin mai

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kungiyar Izala mai hedikwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi karin haske kan maganar ƙarin kudin man fetur.

Sheikh Jingir ya bayyana kafafen yada labaran da suka wallafa maganar inda ya ce su ya kamata a fara zagi kafin a iso kansa.

Malamin ya bayyana dalilin da ya sa mutane suka yi ca a kansa inda ya kare shugaba Tinubu kan karin farashin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.