Sabuwar Matsala Ta Tunkaro El Rufai kan Mulkin da Ya Yi a Kaduna

Sabuwar Matsala Ta Tunkaro El Rufai kan Mulkin da Ya Yi a Kaduna

  • Ƙungiyar SKLC ta mutanen Kudancin jihar Kaduna na son a binciki tsohon Gwamna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai
  • Ƴan ƙungiyar sun zargi tsohon gwamnan na jihar Kaduna da yin mulkin zalunci tare da takurawa mutanen Kudancin Kaduna
  • Sun buƙaci hana shi sake riƙe wani muƙami saboda abin da suka kira gallazawa mutanen yankin da ya yi a lokacin mulkinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƙungiyar Southern Kaduna Leadership Council (SKLC) ta buƙaci a gudanar da binciken shari’a kan ayyukan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai.

Ƙungiyar SKLC ta zargi El-Rufai jagorantar mulkin zalunci a kan mutanen Kudancin Kaduna a lokacin gwamnatinsa.

An bukaci a binciki Nasir El-Rufai
Mutanen Kudancin Kaduna sun taso El-Rufai a gaba Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Ƙungiyar SKLC ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka shirya, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron SKLC ta ƙaryata iƙirarin tsohon mai ba El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, wanda ya ce wasu masarautu, ciki har da Adara, sun nemi a canza musu suna da tsarin shugabancinsu.

SKLC ta taso Nasir El-Rufai a gaba

A cewar Timothy B. Gandu, sakataren SKLC, wannan iƙirarin yaudara ce. Ya bayyana cewa gwamnatin El-Rufai ce ta fara shirin sauya tsarin masarautu ta hanyar kafa kwamitin mutum 13 a shekarar 2017.

Ayyukan wannan kwamitin sun haɗa da bincike da bayar da shawarar yadda za a canza sunayen masarautu waɗanda suka nuna ƙabilanci zuwa sunaye da ke danganta su da wuraren da suke.

Ƙungiyar ta kuma zargi El-Rufai da amfani da kujerar mulkinsa wajen ƙarfafa rarrabuwar kawuna ta fannin addini da ƙabilanci.

Timothy B. Gandu ya ce, a wani faifan bidiyo da ya yaɗu, El-Rufai ya amsa cewa ya yaudari wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyyarsa daga Kudancin Kaduna, tare da ingiza tsarin siyasa na Musulmi da Musulmi tun daga shekarar 2019 a jihar.

“El-Rufai ya yi ƙoƙarin sauya tsarin Kudancin Kaduna ta hanyar ɗaure gindin ƴan bindiga da kuma korar al’ummarmu daga ƙasarsu."

"Ya taɓa cewa a cikin shekara 20, Kudancin Kaduna ba za ta ƙara yin tasiri ba. Wannan maganar ta nuna irin zaluncin da muke fuskanta tsawon lokaci."

- Timothy B. Gandu

Kungiyar na son a bincike Nasir El-Rufai
Kungigar mutanen Kudancin Kaduna na son a binciki El-Rufai Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wane mataki aka buƙaci a ɗauka kan El-Rufai

Ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ba da izinin gudanar da bincike kan laifukan da ake zargin El-Rufai ya aikata yayin mulkinsa.

Sun buƙaci a gayyaci El-Rufai don a bincike shi tare da gurfanar da shi gaban kwamitin binciken shari’a.

Sannan a haramta masa riƙe kowace kujera ta gwamnati nan gaba saboda karya kundin tsarin mulki.

Sun kuma buƙaci hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro su binciki waɗanda ake zargin ya biya kudi don 'hana kashe-kashe'.

El-Rufai ya koka kan shugabannin yanzu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya koka kan irin shugabannin da ke rike da madafun iko a yanzu.

Nasir El-Rufai ya nuna damuwa kan cewa a yanzu ƴan bindiga da ke zaune a birane ke riƙe da madafun iko.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ƴan Najeriya ba su tsayawa su zaɓi mutanen kirki a matsayin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng