Me Ake Kullawa: Wike Ya Gana da Tinubu da Wasu Tsofaffin Gwamnonin PDP

Me Ake Kullawa: Wike Ya Gana da Tinubu da Wasu Tsofaffin Gwamnonin PDP

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya jagoranci wasu tsofaffin gwamnonin jam'iyyar PDP zuwa wajen Shugaba Bola Tinubu
  • Nyesom Wike tare da sauran gwamnonin sun sanya labule da shugaban ƙasan a fadarsa da ke Aso Rock a birnin tarayya Abuja
  • Ganawar tsofaffin gwamnonin da shugaban ƙasan na zuwa ne yayin da ake ta ƙoƙarin shawo kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Nyesom Wike ya jagoranci wasu tsofaffin gwamnonin jam’iyyar PDP guda uku zuwa wani taro tare da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Wike ya gana da Shugaba Bola Tinubu
Wike ya kai tsofaffin gwamnonin PDP zuwa wajen Shugaba Tinubu Hoto: @OlayinkaLere
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta kawo rahoton cewa an gudanar da taron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike da tsofaffin gwamnonin PDP sun gana da Tinubu

Ya taron ya haɗa da wasu aminan Wike daga jam’iyyar PDP da kuma mambobin tsohuwar ƙungiyar G5, wata ƙungiya da ta yi fito na fito da shugabancin jam’iyyar a lokacin shirin zaɓen 2023.

Tsofaffin gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Ayodele Fayose na jihar Ekiti, Samuel Ortom na jihar Benue, da Okezie Ikpeazu na jihar Abia, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayani game da tattaunawar da aka yi ba, ana kallon taron a matsayin wani yunƙuri na sake tsara tsarin siyasa kafin babban zaɓen 2027.

Taron ya gudana ne a ranar Asabar, a daidai lokacin da kwamitin sulhu da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ke jagoranta ke ci gaba da ƙoƙarin shawo kan rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar PDP.

Wike ya jagoranci tsofaffin gwamnonin PDP zuwa wajen Tinubu
Wike da tsofaffin gwamnonin PDP sun gana da Tinubu Hoto: @OlayinkaLere
Asali: Twitter

Ana ƙoƙarin sasanta rikicin PDP

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, ya sanar da nadin Saraki a watan Mayu tare da wasu mutane shida domin neman hanyar warware rikicin da ke barazana ga makomar babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya

Tun kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Wike ne ya jagoranci gwamnonin G5 wajen adawa da PDP da ɗan takararta, Atiku Abubakar.

Gwamnonin sun nuna rashin amincewa da fitowar Atiku a matsayin ɗan takarar jam’iyyar, inda suka dage cewa kamata ya yi a bai wa yankin Kudu damar tsayar da ɗan takara.

Rikicin da ya biyo baya ya sa gwamnonin G5 suka mara wa Bola Tinubu na jam’iyyar APC baya a zaɓen 2023.

Bayan da Tinubu ya yi nasara a zaɓen, ya naɗa Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja.

Wike ya magantu kan sanya sunan Tinubu a ICC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya kare kansa kan sanya sunan Shugaba Bola Tinubu a cibiyar ICC.

Nyesom Wike ya bayyana cewa ko kaɗan bai yi nadama ba kan matakin da ya ɗauka na sanya sunan shugaban ƙasan.

Ya bayyana cewa masu sukar kuɗaɗen da aka kashe wajen gyara cibiyar, ba su san abu mai kyau ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng