Mutuwa Ta Ziyarci Gidan Marigayi Sheikh Giro Argungu, Dansa Ya Rasu
- Allah ya yi wa Abdulmannan Abubakar Giro Argungu rasuwa a garin Argungu, Jihar Kebbi, bayan gajeruwar rashin lafiya
- Rahotanni sun tabbatar da cewa za a gudanar da jana’izarsa yau Asabar da karfe 2:00 na rana a Masallacin Idi na garin Argungu
- Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana jimaminsa tare da fatan Allah ya saka masa da Aljanna tare da mahaifinsa da sauran magabata
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Rahotanni daga Jihar Kebbi sun tabbatar da rasuwar Abdulmannan Abubakar Giro Argungu, wanda da ne ga marigayi Sheikh Giro.
Iyalan marigayin sun bayyana cewa Abdulmannan ne mai kula da shafin Sheikh Dr Abubakar Giro Argungu a kafar sada zumunta.

Asali: Facebook
Shafin Sheikh Giro ya wallafa a Facebook cewa ya rasu ne a yau Asabar bayan gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a Masallacin Idi da ke cikin garin Argungu, inda ake sa ran dubban jama’a za su halarta domin yi masa sallah.
Dan Sheikh Giro ya yada ilimin Musulunci
Abdulmannan ya kasance ɗan marigayi Sheikh Abubakar Giro, kuma ya taka rawa sosai wajen ci gaba da yada ilimin mahaifinsa ta kafar Facebook da sauran hanyoyin zamani.
A lokacin azumin Ramadan da ya gabata, ya dauki nauyin yada tafsirin Sheikh Isa Ali Pantami daga Masallacin Annoor da ke Abuja zuwa gidan rediyon Nagari FM da ke Birnin Kebbi.
Wannan aiki ya sa da dama suka yaba da kishinsa da sadaukarwarsa wajen yada ilimi da kalmar Allah.
Pantami ya yi ta’aziyya ga iyalai da al’umma
Fitaccen malami kuma tsohon ministan sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami, ya bayyana alhini da jimami bisa wannan babban rashi.
A wata wallafa da ya yi a Facebook, ya ce:
“Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un! Muna mika taaziyyar rasuwar Malam AbdulMannan Abubakar Giro Argungu, wanda ya ke ɗa ga Shaykh Abubakar Giro Argungu (RH).
Muna rokon Allah ya sanya Aljannah ce makomarsa tare da mahaifinsa da sauran magabatanmu gaba ɗaya.”

Asali: Facebook
Jama’a na masa addu’a a kafafen sada zumunta
Bayan sanar da rasuwar Abdulmannan, jama’a da dama daga sassa daban-daban na ƙasar nan sun shiga kafafen sada zumunta suna yin addu’ar Allah ya gafarta masa.
Wasu daga cikin su sun bayyana cewa ya taka rawar gani a rayuwarsa, kuma rayuwarsa ta zama abar koyi ga matasa.
Ana sa ran cewa jana’izarsa za ta samu halartar malamai, iyalai, abokai da sauran jama’a daga sassa daban-daban.
Sarki ya yabawa Sheikh Pantami a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Hakimin Pantami a jihar Gombe ya yaba da kokarin da Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ke yi.
Hakimin ya bayyana haka ne a cikin wata takarda da ya fitar tare da bayyana muhimman rawar da malamin ya taka a Gombe da Najeriya baki daya.
Jama'a da dama sun yaba da kokarin da Hakimin Pantami ya yi na fitowa fili ya yabi mutumin da suka ce aka san shi da taimako.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng