An Yi Kuskure kan Rera Taken Najeriya Ranar Dimukraɗiyya? An Gano Gaskiya
- An yi ta yada wani bidiyo da aka ce ba a rera sabon taken kasa ba yayin jawabin Bola Tinubu a ranar dimokradiyya a majalisa
- Sai dai binciken kwakwaf ya tabbatar da cewa an rera taken Najeriya sau biyu, kafin da bayan jawabin Bola Tinubu
- Bidiyon da ya yadu wanda aka yanke shi don kada a nuna inda aka rera taken; hakan ya tabbatar maganar da ke yawo ba ta da tushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An yada wani rubutu hade da faifan bidiyo kan cewa ba a rera sabon taken Najeriya ba a ranar dimukraɗiyya.
Bidiyon ya karade kafofin sadarwa wanda ya sanya shakku da tambayar ko an sauya taken Najeriya ne.

Asali: Twitter
Zargin rashin rera taken Najeriya ranar dimukraɗiyya
Wanda ya wallafa rubutun mai suna @OurFavOnlineDoc, ya yada bidiyo na daƙiƙa 50 da ke nuna Tinubu yana magana a gaban ‘yan majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon wanda ya karade dandalin X ya yi ikirarin cewa ba a rera sabon taken kasa ba yayin bikin dimokradiyya a majalisar tarayya.
An yi rubutu a saman bidiyon kamar haka:
“Wannan bidiyon na nuna lokacin kafin da bayan jawabin Bola Tinubu.
“A ranar dimokradiyya, ba a yi amfani da taken kasa ba. Sai dai ‘On your mandate’ aka rera da babu hankali da tunani.”
Najeriya ta yi bikin cika shekaru 26 na mulkin dimokradiyya ba a ranar 12 ga Yunin 2025.
Tinubu, wanda a farko aka shirya zai gabatar da jawabi, ya soke hakan amma ya yi magana a zaman hadin gwiwa na majalisa.
A lokacin jawabin, ya karrama wasu 'yan Najeriya, ciki har da matattu da suka taka rawa wajen tabbatar da dimokradiyya.

Asali: Facebook
Shin an rera taken Najeriya a majalisa?
TheCable ta duba cikakken bidiyon tsawon sa'o'i biyu da aka ɗora a tashar majalisa a YouTube.
A daidai minti 3 da daƙiƙa 54 cikin bidiyon, rundunar tsaro ta fara rera taken kasa bayan shigowar Tinubu.
Daga bisani, a 1:33:06 cikin bidiyon, an sake rerawa bayan daukar hoto, kafin Tinubu ya yi bankwana da ‘yan majalisar.
Bidiyon da ke yawo an gyara shi ta yadda aka yanke bangarorin da aka rera taken kasa sau biyu.
Maganar cewa ba a rera taken kasa ba a bikin ranar dimokradiyya da aka gudanar a majalisa ba ta da tushe gaskiya.
Bidiyo na gaskiya ya nuna an rera taken kasa a farkon zaman hadin gwiwa da kuma a karshensa.
Ranar dimukraɗiyya: Tinubu ya ba da hakuri
Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya lissafa sunayen mutane biyu da ke raye a cikin jerin matattun da aka karrama a jawabin ranar dimokuraɗiyya.
Fadar shugaban ƙasa ta bakin Bayo Onanuga ta fitar da sanarwar neman afuwar jama'a, tana mai cewa ba ayi kuskuren da gangan ba.
An tabbatar da cewa za a gyara sunayen da aka bayar a shafukan gwamnati, yayin da aka jaddada girmamawa ga waɗanda aka ambata.
Asali: Legit.ng