Kwankwaso Ya Tsawatar, Ya Shiga Tsakanin Rikicin Dan Majalisa da Kakakin Abba
- Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga tsakani domin kawo karshen sabanin Tijjani Abdulkadir Jobe da Sunusi Bature Dawakin Tofa
- Ana tunanin rikicin ya samo asali ne daga cece-kuce kan wanda ya dace ya wakilci Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa a 2027
- Tuni Sanusi Bature ya bayyana cewa komai ya wuce, kuma yanzu lokaci ne na mayar da hankali wajen ci gaban jam'iyyar NNPP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga tsakani don warware takaddama tsakanin ‘yan jam’iyyar NNPP.
'Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Tofa/Dawakin Tofa/Rimin Gado, Hon. Tijjani AbdulKadir Jobe da Kakakin Gwamna, Sanusi Bature Dawakin sun rika nunawa juna yatsa.

Asali: Facebook
A sanarwar da Sanusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya tabbatar da cewa Sanata Kwankwaso ya gayyace shi da Hon. Jobe kan musayar yawu dake tsakaninsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya kira Jobe da Sanusi D/Tofa
Mashawarcin gwamnan Kano kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa an yi zaman sasancin a ranar Alhamis, a gidan Kwankwaso da ke Abuja
A cewar Sanusi Bature Dawakin Tofa:
"Na samu gayyata zuwa Abuja daga Magudun siyasar Najeria a yayin da nake kasar Kenya domin halartar wani taro."
"Kuma na amsa wannan gayyata a daren yau domin yin zaman sulhu da dan'uwa na Hon. Tijjani Jobe bisa jagorancin Madugu Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso."
Kwankwaso ya sulhunta Sanusi da Jobe
Sanusi Bature ya ce tuni aka samu nasarar sulhun, kuma baki dayansu sun amince da a ci gaba da yiwa jam'iyyar NNPP aiki a Kano.

Asali: Facebook
A kalamansa:
"Muna kira ga magoya baya da a daina cin zarafin juna kasancewar mu 'yan jam'iyayyar NNPP Kwankwasiyya."
"Dukkannin mu, mun yiwa Magudu alkawari zamu cigaba taimakon 'yan jam'yya tare bujiro da bukatun mu cikin mutunta juna, kyautatawa da aminci kamar yadda muke yi a baya."
"Allah ya taimake mu, da jam'iyyarmu, da jagorinmu a koda yaushe."
"Inda muka yi daidai, Allah ya bamu lada, inda kuma muka yi kuskure Allah ya yafe mana."
Asalin takaddama tsakanin Sanusi da Jobe
Takaddamar ta samo asali ne daga sabanin ra’ayi kan wanda ya fi cancanta ya tsaya takarar majalisar tarayya mai wakiltar Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa a zaben 2027.
Hon Sunusi Bature na ganin lokaci ya yi da za a sauya fasalin wakilci, yana mai zargin Hon Jobe da rashin tabuka abin azo a gani cikin fiye da shekaru 18 da ya shafe a kujerar.
Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin magoya bayansu, inda a baya-bayan nan Hon Jobe ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya yi hankali da Sunusi Bature kan zargin zagon kasa.
Rikici ya ruru tsakanin dan majalisa da Sanusi
A baya, mun wallafa cewa Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe ya yi zargin mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, da cin amanar jam'iyyar NNPP.
A cikin wani bidiyo, an hango Hon Jobe a fusace, inda ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya dakatar da hulɗarsu da Sanusi Bature saboda yiwa jam'iyya zagon kasa.
A cikin jawabansa, ya ce Sanusi Bature Dawakin Tofa na karbo kudi daga APC, yana kuma kokarin korar dukkanin yan NNPP na hakika a Dawakin Tofa da kewaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng