'Dan Majalisar Kano Ya Zargi Kakakin Abba Gida Gida da Hada Kai da Su Ganduje
- 'Dan majalisar tarayya, Tijjani AbdulKadir Jobe ya gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf kan cigaba da mu'amala da Sanusi Bature Dawakin Tofa
- Hon Jobe, wanda dan majalisar yankin Sanusi ne, yana zargin hadimin Abba da hada kai da 'ya'yan tsohon gwamna Abdullahi Ganduje
- Ya ce Sanusi na karbo kuɗi daga bangaren Ganduje da kuma korar 'yan NNPP a mazabunsu, wanda ya ce zai iya cutar da jam’iyyar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Dan majalisar tarayya Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe, ya gargadi gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, kan mu'amalarsa da Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Dan majalisar mai wakiltar mazabun Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa a jihar Kano, ya zargi Sanusi Bature Dawakin Tofa, Darakta Janar na Yada Labarai a gidan gwamnatin Kano, da cin amanar NNPP.

Asali: Facebook
Gargadin na Jobe yana kunshe ne a cikin wani bidiyo da tsohon hadimin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wato Hassan Cikinza Rano ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: Zarge-zargen da Jobe ke yi wa Sanusi
A cikin bidiyon, Hon. Abdulkadir Jobe ya zargi Sanusi Bature Dawakin Tofa da hada kai da ’ya’yan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da Gwaggo.
A cewarsa:
"Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, idan har zaka ci gaba da mu'amala da Sanusi Bature Dawakin Tofa a matsayin mai magana da yawunka, sannan ya dawo nan gidanmu na Dawakin Tofa da Rimin Gado, yana hada kai da su Abba Ganduje da ’ya’yan Ganduje da Gwaggo — to wannan na nuna kai ne ka tura shi ya hada kai da su."
Ya ci gaba da cewa Sanusi Bature Dawakin Tofa yana hana bayyana wa Ganduje yabo, duk da adawar da ke tsakaninsu.
Kano: Sauran zarge-zargen Jobe kan Sanusi
Hon. Jobe ya kuma kara da cewa Sanusi Bature yana karbar kudi daga wajen ’yan bangaren Ganduje, wanda wani kusa da Jobe ya bayyana a matsayin “kwangila.”

Asali: Facebook
Ya kuma zarge shi da korar wasu ’yan NNPP a yankin Dawakin Tofa, abin da Jobe ya ce na iya janyo wa jam’iyyar cikas a siyasa a yankin.
A kalamansa:
"Yana karbar kudi daga gurinsu. Mai girma gwamna, ina kira gare ka da ka kira na musamman."
"In har siyasar ka ke kuma siyasar ci gaban Dawakin Tofa kake yi, to Sanusi ba ya wakiltarka."
Jobe ya ce siyasar da Sanusi Bature ke yi ba ta wakiltar Gwamna Abba Kabir Yusuf ko Rabiu Musa Kwankwaso.
"Sanusi Dawakin Tofa, in har dan jam’iyyarmu ne, daga yau ya daina korar ’yan jam’iyyarmu na NNPP, kuma ya daina yabawa Abba Ganduje."
Rikici ya balle tsakanin Sanusi da Jobe
A baya, kun ji cewa NNPP ta tabbatar da barkewar saɓani a tsakanin mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, da ɗan majalisar tarayya, Abdulkadir Jobe.
An jiwo Sanusi Bature yana zargin Abdullahi Jobe da gaza sauke nauyin jama'a da ya rataya a wuyansa a majalisar wakilai, inda ya ce dole ne a fada masa gaskiya kan gazawarsa.
A kalamansa, Shugaban NNPP na Kano, Dr. Hashim Dungurawa ya ce sabanin ya samo asali kam kujerar Jobe, amma suna duk abin da ya dace domin shawo kan matsalar.
Asali: Legit.ng