"Ba Laifin Fubara ba ne," Yan Majalisa Sun Yi Magana kan Yiwuwar Gwamna Ya Koma APC

"Ba Laifin Fubara ba ne," Yan Majalisa Sun Yi Magana kan Yiwuwar Gwamna Ya Koma APC

  • Kungiyar ƴan Majalisun jam'iyyun adawa ta ce bai kamata a ga laifin dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ba idan ya koma APC
  • A cewar ƴan majalisun, PDP ta gaza kare gwamnan wanda ya tsinci kansa a cikin matsala sakamakon rikicinsa da Nyesom Wike
  • An fara yaɗa jita-jitar cewa Fubara na iya tsallaka wa daga PDP zuwa APC bayan ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Ƙungiyar ‘yan Majalisun jam’iyyun adawa a Najeriya ta ce bai kamata a ga laifin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ba idan har ya yanke shawarar sauya sheƙa zuwa APC.

Ƴan Majalisun tsagin adawa sun ce babu wani dalili da zai sa a ga laifin Gwamna Fubara, wanda aka dakatar na tsawon watanni shida, saboda PDP ta ci amanarsa.

Dakataccen gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara.
Yan majalisun jam'iyyun adawa sun ce ba wani abu bane idan Fubara ya koma APC Hoto: Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Leadership ta tattaro cewa ‘yan majalisun sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsu, Hon. Ikenga Ugochinyere, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana jita-jitar Fubara zai bar PDP zuwa APC

Sun faɗi haka ne a matsayin martani kan jita-jitar cewa Gwamna Fubara na shirin sauya sheƙa zuwa APC bayan ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Legas.

Sanarwar ta ce PDP ta mika duka iko da tsarin jam’iyya na Ribas ga tsohon gwamna kuma Ministan Abuja a yanzu, Nyesom Wike, wanda ke cikin gwamnatin APC.

‘Yan majalisun sun ce PDP ta marawa wasu ‘yan majalisa da suka sauya sheƙa daga cikin ta zuwa APC baya, duk kuwa da cewa suna ƙoƙarin tsige Gwamna Fubara.

Ƴan Majalisun adawa sun caccaki PDP

A cewarsu, babu wani mataki da jam’iyyar PDP ta ɗauka na kare gwamnan, illa wasu kalamai da jam'uyyar ta yi wanda suka saɓa wa juna, rahoton Daily Post.

“Jita-jita ta fara yawo cewa Gwamna Siminalayi Fubara, wanda aka dakatar bayan ayyana dokar-ta-baci a jihar Ribas, na shirin sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
"Wannna jita jita ta ƙara ƙamari ne bayan ziyarar da dakataccen gwamnan ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Legas.”
“To, idan har Gwamna Fubara ya sauya sheƙa zuwa APC, bai kamata a zarge shi ko a ga laifinsa ba, laifin PDP ne, wadda ta mika tsarin jam’iyyar a hannun tsohon gwamna kuma minista a gwamnatin APC, Nyesom Wike.

- In ji sanarwar.

Gwamna Fubara da Wike.
Yan Majalisun tsagin adawa sun ce PDP ta gaza kare Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

An zargi PDP da gaza kare Siminalayi Fubara

Ƴan Majalisun jam'iyyun adawa sun caccaki PDP da cewa ba ta yi wani yunkurin baiwa Fubara kariya ba, sai dai ta soki Shugaba Tinubu daga baya kuma ta goyi bayansa.

Ƙungiyar ta kuma caccaki shugabancin PDP bisa zargin rashin nuna kishin ɗan jam’iyyarsu da ke cikin matsala, tare da bayyana cewa jam’iyyar na nuna bangaranci da son rai.

APC ta gargaɗi Fubara kan batun tsige shi

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi gargaɗin cewa ƙoƙarin yin sulhu na gaskiya ne kawai zai hana a tsige Sir Siminalayi Fubara daga kan muƙaminsa.

Shugaban APC na Ribas, Tony Okocha ya bayyana cewa har yanzu dakataccen gwamnan bai yi wani yunƙuri domin yin sulhu da ƴan majalisar dokokin Ribas ba.

Kalaman Tony Okocha na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Shugaba Tinubu zai iya dawo da Fubara kan muƙaminsa na gwamna a ranar dimokuraɗiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262