Jam'iyyar APC Ta Samo Mafita ga Gwamna Fubara kan Yunkurin Tsige Shi

Jam'iyyar APC Ta Samo Mafita ga Gwamna Fubara kan Yunkurin Tsige Shi

  • Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Rivers ta ja kunnen Gwamna Siminalayi Fubara wanda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar
  • Shugaban APC a Rivers, Tony Okocha, ya bayyana cewa dole ne gwamnan ya zo ya bi hanyar yin sulhu idan yana son ya tsira daga tsigewa
  • Okocha ya nuna cewa har yanzu babu wani yunƙuri da dakataccen gwamnan ya yi domin yin sulhu da zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokokin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Jam'iyyar APC ta reshen jihar Rivers ta ja kunnen dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara.

Jam'iyyar APC ta yi gargaɗin cewa ƙoƙarin yin sulhu na gaskiya ne kawai zai hana a tsige gwamnan daga kan muƙaminsa.

Jam'iyyar APC ta gargadi Gwamna Fubara
APC ta ba Gwamna Fubara shawara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Rivers, Tony Okocha, ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai ranar Talata a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tony Okocha ya bayyana cewa dakataccen gwamnan bai yi wani yunƙuri ba domin yin sulhu da zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokokin jihar.

Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a Rivers

A ranar 18 ga Maris, Shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers saboda rikicin siyasa da ke tsakanin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da Gwamna Siminalayi Fubara.

Biyo bayan ayyana dokar ta ɓacin, shugaban ƙasa ya dakatar da Gwamna Fubara da kuma ƴan majalisar dokokin jihar.

Shugaba Tinubu ya kuma naɗa tsohon babban hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya), a matsayin shugaban riƙo na tsawon watanni shida.

Duk da cewa gwamnonin jam’iyyar PDP sun je kotu kan wannan matakin da shugaban ƙasa ya dauƙa, ganawar da aka riƙa yi tsakanin Tinubu, Wike da kuma Gwamna Fubara da aka dakatar, sun nuna yiwuwar fara samun sulhu a tsakaninsu.

Wane gargaɗi APC ta yi wa Gwamna Fubara?

Gargaɗin Tony Okocha ya zo ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Shugaba Tinubu zai iya dawo da Fubara kan muƙaminsa a bikin ranar dimokuraɗiyya na 12 ga watan Yunin 2025.

APC ta ja kunnen Gwamna Fubara
APC ta ce Fubara bai bi hanyar neman sulhu ba Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook
"Zan iya tabbatar muku da cewa babu wani yunkurin sulhu da ake yi a halin yanzu a jihar Rivers."
“Gwamnan da aka dakatar, Fubara, bai ɗauki ko da ƙaramar hanyar sulhu da ƴan majalisar jihar ba."
“Sahihin sulhu shi ne kawai zai cece shi daga tsigewa, domin hukuncin Kotun Koli yana nan daram."

- Tony Okocha

Gwamna Fubara ya yabawa Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Fubara wanda aka dakatar daga kan muƙaminsa ya yabawa Shugaba Tinubu ne kan dokar ta ɓacin da ya sanya a jihar Rivers.

Simi Fubara ya bayyana cewa sanya dokar ta ɓacin da shugaban ƙasan ya yi, ta hana jihar faɗawa cikin rikicin siyasa wanda zai iya jawo durƙushewarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng