Jigo a SDP Ya Fadi Taimakon da Masu Komawa APC Ke Yi Wa 'Yan Najeriya
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya taɓo batun masu sauya sheƙa zuwa APC
- Adebayo ya nuna cewa masu komawa jam'iyyar APC na sauƙaƙawa ƴan Najeriya wajen gano inda matsalarsu take
- Ya nuna cewa ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da basirar da yake da ita wajen kyautata rayuwar ƴan Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Prince Adewole Adebayo, ya yi magana kan sauya sheƙar da ƴan siyasa ke yi zuwa APC.
Adewole Adebayo ya ce sauya sheƙar da ƴan siyasa ke yi zuwa APC ya sauƙaƙa wa ƴan Najeriya gane waɗanda ke da hannu a cikin wahalhalun da suke ciki.

Asali: Facebook
Adewole Adebayo ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon SDP ya ƙalubalanci Bola Tinubu
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya maida ƙwarewarsa ta siyasa zuwa kyautata rayuwar ƴan Najeriya.
“Ka ga, duk wannan dabarar siyasa da ake magana a kai tana amfani ne yayin da mutum ke neman mulki. Kana neman mulki ne domin ka yi wa mutane aiki.”
“Mutane na mutuwa saboda yunwa. Rashin tsaro ya yi ƙamari. Duk lokacin da ka karanta jarida, sai ka ji baƙin ciki domin kana fatan samun labari mai daɗi, amma ba ka samu."
"Kana so ka karanta labari mai daɗi, ba na kashe-kashe da tashin hankali ba. Don haka, idan shugaban ƙasa yana da basira, ya yi amfani da ita wajen tafiyar da rayuwar ƴan Najeriya."
- Adewole Adebayo
Adebayo ya magantu kan masu komawa APC
Da aka tunatar da shi cewa yawaitar sauya sheƙa daga zuwa APC na iya nuna cewa wani abu mai kyau na faruwa a jam'iyyar, sai ya ce wannan sauya sheƙar za ta taimakawa ƴan Najeriya wajen gane masu hannu a cikin wahalhalunsu.

Asali: Facebook
Adewole Adebayo ya ce sauya sheƙar ta tattara mutane masu tunani iri ɗaya, kuma waɗanda suka ɓarnatar da albarkatun ƙasa na taruwa wuri guda domin ƴan Najeriya su iya ganesu cikin sauƙi.
"Waɗanda ake zargi sun haɗu wuri guda. Ka ga, suna sauƙaƙawa al’umma fahimtar inda matsalarsu ta ke."
"Abin da nake gani shi ne, mutanen da ke ɓata tafiyar ƙasar nan suna cikin jam’iyyu daban-daban. Amma saboda wani dalili, domin sauƙaƙawa ƴan Najeriya, dukkaninsu yanzu suna taruwa a jam’iyya ɗaya."
- Adewole Adebayo
Adewole ya ce ba zai janyewa Atiku ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya bayyana cewa ba zai iya janyewa Atiku Abubakar takara ba.
Adewole ya bayyana cewa ba zai haƙura ya bar Atiku ya yi takarar shugaban ƙasa ba idan suka haɗu a jam'iyya ɗaya.
Ya bayyana cewa zai yi hakan ne duk kuwa da irin girmamawar da yake yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng