Siyasa Mugun Wasa: Reno Omokri Ya Fara Maganar Sulhu tsakanin Atiku da Tinubu

Siyasa Mugun Wasa: Reno Omokri Ya Fara Maganar Sulhu tsakanin Atiku da Tinubu

  • Tsohon hadimin shugaban Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce bai kamata ya caccaki Atiku Abubakar ba saboda alherin da ya yi masa
  • Omokri ya ce ko da yake yana goyon bayan Bola Tinubu, hakan ba zai hana shi mutunta Atiku ba saboda wata kyakkyawar alaka da suka taɓa yi
  • Ya kuma bayyana burinsa na ganin an sasanta tsakanin Atiku da Tinubu, yana mai cewa har yanzu yana mutunta Wazurub Adamawa matuƙa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon hadimin Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya fadi dalilin da ya sa yake sukar wasu 'yan adawa kamar Peter Obi da Nasir El-Rufa’i amma baya sukar Atiku Abubakar.

A cikin wata amsa da ya bayar ga masu bibiyar sa a kafafen sada zumunta, Omokri ya ce ba zai caccaki Atiku ba duk da cewa yana goyon bayan Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC.

Atiku
Reno ya ce yana fatan sulhu tsakanin Atiku da Tinubu. Hoto: Reno Omokri|Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Reno Omokri ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Reno, da ya fito daga jam’iyyar PDP, ya ce Atiku mutum ne da ya taɓa nuna masa ƙauna da taimako, kuma bai dace ya rama hakan da sukar sa ba.

Atiku ya taimakawa Reno Omokri a rayuwa

Reno Omokri ya bayyana cewa yana da cikakken dalili da ya sa baya sukar Atiku, wanda ya kira da “Waziri”.

Ya ce Atiku ya taɓa taimaka masa a lokacin da yake bukata, kuma hakan ya zamo babban alheri da ba zai taɓa mantawa da shi ba.

Ya ce:

“Ba zan iya sukar Waziri Atiku Abubakar ba saboda na amfana da shi ƙwarai, kuma ban jin kunya in faɗi hakan a bainar jama’a.
"Mutum ne wanda ya taɓa nuna min gaskiya da ƙauna. Duk yadda lamarin ya kaya, ba zan iya canza wannan tunani a kan sa ba.”

Reno na mutunta Atiku duk da son Tinubu

Duk da cewa Omokri ya nuna goyon bayansa ga Tinubu, har ma ya ce zai yaɗa manufofin gwamnatinsa, ya ƙara jaddada cewa hakan ba zai hana shi ci gaba da girmama Atiku ba.

Ya ce:

“Ko Waziri ya kira ni wawa, zan ba shi haƙuri ne, kuma zan ci gaba da girmama shi kamar yadda na saba. Idan ya fadi abu da ban yarda da shi ba, ba zan mayar da martani a fili ba.”
Reno Omokri
Omokri ya ce zai cigaba da girmama Atiku. Hoto: Reno Omokri
Asali: Facebook

Reno na son sulhu tsakanin Atiku da Tinubu

Reno Omokri ya bayyana burinsa na ganin sulhu da zama inuwar siyasa daya ya samu tsakanin Atiku da Tinubu.

Ya ce a matsayinsa na ‘Oton-Olu’ daga yankin Delta, bai dace ya zagi mutumin da bai taɓa cutar da shi ba, ko da kuwa magoya bayansa ne suka cutar da shi.

Ya ce:

“Burina mafi girma yanzu shi ne ganin an haɗa Atiku da Tinubu. Mutunci da sadaukarwa sun fi siyasa muhimmanci a rayuwa,”

APC ta amince da tazarcen Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC a Arewa ta Tsakiya ta shirya taron nuna goyon baya ga Bola Ahmed Tinubu.

A yayin taron, gwamnoni 5 na yankin da tarin magoya bayansu sun bayyana cewa sun amince da tazarcen Tinubu a 2027.

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce Bola Tinubu ya kawo manufofi masu kyau Najeriya kuma an fara cin ribar tsare tsarensa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng