"Ina Tsaye a kan Baka Ta," Naja'atu Muhammad Ta Kalubalanci Nuhu Ribadu Ya Tafi Kotu

"Ina Tsaye a kan Baka Ta," Naja'atu Muhammad Ta Kalubalanci Nuhu Ribadu Ya Tafi Kotu

  • Hajiya Naja’atu Muhammad ta jaddada cewa ba ta yi karya ba, kuma babu abin da zai sa ta janye kalamanta a kan Nuhu Ribadu
  • Ta bayyana cewa kalaman da ta jingina wa Nuhu Ribadu sun tabbata, domin har yanzu suna nan a shafukan yanar gizo
  • Hajiya Naja’atu ta kalubalanci Mashawarcin Shugaban kasa da ya kai ta kotu idan ya na ganin ta yi masa ba daidai ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - 'Yar gwagwarmaya, Hajiya Naja'atu Muhammad ta yi martani ga umarnin da Mashawarcin Shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ba ta.

A yammacin Talata ne Nuhu Ribadu, ta bakin lauyansa ya bayyana rashin jin dadin kalaman zargin shugaba Bola Tinubu da rashawa, wanda Hajiya Naja'atu ta jingina masa.

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Ribadu
Naja'atu Muhammad ta yi martani ga Nuhu Ribadu Hoto: Imam Maleek Auwal Warure/Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

A martanin ta da aka wallafa a shafin Facebook na Premier radio, 'yar gwagwarmayar ta bayyana cewa babu inda ta yi karya a kalamanta, saboda haka ba za ta janye ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kara da cewa ita kawai karin bayani ta nemi Nuhu Ribadu ya yi a kan kalamansa, saboda haka babu abin da zai sa ta karyata kanta.

"Ba karya na yi ba," Naja'atu Muhammad

Hajiya Naja'atu Muhammad ta bayyana cewa babu laifin da ta yi wa Nuhu Ribadu da zai sa ta ba shi hakuri, inda ta dage a kan cewa dukkanin abin da ta fada, gaskiya ne.

A cewar ta:

"To me na yi masa da zan ba shi hakuri? Kai ka taba jin mutum ya fadi gaskiya, ya janye? Abin duk da na fada, ina tsaye a kan baka ta."

"Akwai shaidar kalaman Nuhu Ribadu," Naja'atu

Guda daga cikin 'yan siyasa masu zazzafan ra'ayin a samar da canji a Arewa, Naja'atu Muhammad ta bayyana cewa ba da ka ta fadi magana a kan Nuhu Ribadu ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Naja'atu: Ribadu ya dauki zafi, ya ba 'yar gwagwarmayar wa'adi kan bata suna

Ta ce:

"Abin da na fada shi ne, Nuhu Ribadu da bakinsa, har yanzu kuma maganan nan ta na nan a youtube. Kowa ya duba ya gani.
Lokacin shi Nuhu Ribadu ya na shugaban hukumar EFCC, ya ce Asiwaju Bola Tinubu, ya na daga cikin manya-manyan masu cin rashawa da hanci, wanda za a nuna wa duniya , a fada wa sarki.
Ya ce kuma a gwamnoni na Najeriya, Tinubu shi ne lamba 1 a kan cin rashawa da cin hanci.

Naja'atu Muhammad ta kalubalanci Nuhu Ribadu

'Yar siyasa a Arewacin Najeriya, ta bayyana cewa tun da abin da Ribadu ya fada ta ke maimaita wa, babu abin da zai sa ta warware kalamanta na zarginsa da aikin zuga Tinubu bayan ya soke shi a baya.

Hajiya Naja'atu ta kalubalance shi da cewa:

"Don Allah, don Annabi Nuhu Ribadu ya kai ni kotun koli ta Najeriya. Ba dai kotun Tinubu ba ce? Don Allah, don Annabi ya kai ni. Ina tsaye a kan baka ta.

Kara karanta wannan

"Abin da ka shuka shi za ka girba": Za a rataye mutum 5 har lahira a jihar Kano

Nuhu Ribadu ya gargadi Naja'atu Muhammad

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai ba Shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ta hannun lauyansa, Dr. Ahmed Raji, SAN, ya gargadi 'yar siyasa, Naja'atu Muhammad.

A cikin wani bidiyo, Hajiya Naja’atu ta zargi Ribadu da yin aiki tare da Bola Tinubu, wanda a baya, a lokacin da yake shugabancin Hukumar EFCC, ya ce Tinubu ya kware a cin hanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.