Kama Farfesa Usman Yusuf Ya Kara Tayar da Ƙura, Naja'atu da Ministan Buhari Sun Tona Asiri

Kama Farfesa Usman Yusuf Ya Kara Tayar da Ƙura, Naja'atu da Ministan Buhari Sun Tona Asiri

  • Ƴar gwagwarmaya, Naja'atu Mohammed da tsohon minista, Solomon Dalung sun nuna ɓacin ransu kan ci gaba da tsare Farfesa Usman Yusuf
  • Naja'atu ta yi ikirarin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta kama tsohon shugabam NHIS ne domin ta rufe bakin masu faɗa maya gaskiya
  • Dalung ya bayyana cewa abin mamakin shi ne kuɗin da ake tuhumarsa ba su kai adadin da hukumar EFCC ta ce ya taimaka an ƙwato ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kama tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa watau NHIS, Farfesa Usman Yusuf na ci gaba da jan hankalin manyan mutane.

Tsohon ministan matasa da wasanni, Salomon Dalung da fitacciyar ƴar gwagwarmayar nan, Naja'atu Mohammed sun nuna ɓacin ransu kan lamarin.

Naja'atu Mohammed da Salomon Dalung.
Naja'atu Muhammed da Salomon Dalung sun nuna damuwa kan kama Farfesa Usman Yusuf Hoto: Naja'atu Mohammed, Barrister Solomon Dalung
Asali: Facebook

A wani faifan bidiyo da Hausa Fulani Blog ya wallafa Facebook, Naja'atu ta zargi gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ƙoƙarin tozarta masu faɗa mata gaskiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naja'atu Mohammed ta soki gwamnati

Naja'atu, wacce ta jaddada cewa gadon gwagwarmaya ta yi, ta ce gwamnatin tarayya ta kama Farfesa Usman ne ba don komai ba sai don ta tozarta shi.

Ƴar gwagwarmayar ta yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan kammala zaman kotu a Abuja, wanda aka hana belin Farfesa Yusuf yau Laraba.

Naja'atu Mohammed ta yi kira ga ƴan Arewa su tashi tsaye su nemi adalci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, tana mai cewa ba su da uwa da uba a wannan gwamnatin.

"Ba don Allah aka kama Farfesa Yusuf ba"

"Ba a nemi a kama shi (Farfesa Usman Yusuf) ba sai don a rufe bakin masu faɗawa gwamnati gaskiya, don haka ya kamata gwamnatin Tinubu ta sani Allah ya halicce mu ne a kan yaki da zalunci."
"A kan maganar Farfesa, shin tun yaushe ya bar (hukumar NHIS)? Me ya sa tun tuni yau shekara tara ba su neme shi ba sai da ya fara cewa abin da gwamnati take yi musamnan ga ƴan Arewa ba daidai ba ne.

"Sai a wannan lokacin, ka ga kenan ba don Allah aka kama shi ba, kuma ba don ya yi laifi aka kama shi ba."

- In ji Naja'atu Mohammed.

Naja'atu ta buƙaci ƴan Arewa su buɗe idonsu, tana mai cewa idan yau an kama Farfesa Yuauf, mai yiwuwa ita za a damƙe gobe.

Dangane da zaman kotu, Naja'atu Mohammed ta bayyana cewa suna bukatar a yi adalci a bayar da belin Farfesa Usman Yusuf.

Tsohon ministan Buhari ya yi magana

A nasa jawabin, tsohon minsita, Solomon Dalong ya ce suna fatan a zaman da kotu za ta yi ranar 27 ga watan Fabrairu, za a bayar da belin Farfesa Usman Yusuf.

A cewarsa, kuɗin da hukumar EFCC ke zargin tsohon shugaban NHIS ɗin ya yi sama da faɗi da su, ba su kai waɗanɗa ya taimaka masu suka kwato ba.

"Za mu bi doka, so muke mu kure su, idan ka duba kuɗin da suke tuhumarsa bai kai wanda suka ce ya taimaka an kwato ba, ka ga nan akwai lauje cikin naɗi," In ji Dalung.

Akasarin ƴan Arewa sun yi tir da wannan lamari, Umar Kabir, malamin makaranta a Katsina ya shaidawa Legit Hausa cewa gwamnati mai ba ta son adawa.

A cewarsa, ƙiri-kiri an nuna cewa Arewa za a yaƙa domin kama mutum kamar Farfesa Usman Yusuf, ba shi a karan kansa kaɗai ake son tozartawa ba.

"Kai tsaye Arewa ake son a yi wa illa, domin alamu sun nuna duk wanda zai ɗaga murya idan an cuce mu, gwamnati ba za ta barshi ya zauna lafiya ba," in ji shi.

Kotu ta hana belin Farfesa Yusuf

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun birnin tarayya Abuja ta yi fatali da bukatar bayar da belin tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf.

Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa ce ta gurfanar da Farfesan a gaban kotu, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara a faɗin ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262