Saraki: Ba daidai ba ne ayi gum yayin da ake samun sabani da Makiyaya a Ondo da Oyo

Saraki: Ba daidai ba ne ayi gum yayin da ake samun sabani da Makiyaya a Ondo da Oyo

- Bukola Saraki ya yi magana game da abubuwan da ke ta faruwa a Ondo da Oyo

- ‘Dan siyasar ya ce tsaro ya na ta tabarbarewa, ya yi kira ayi maza a tashi tsaye

- Saraki yana cewa bai kamata masu ruwa-da-tsaki duk suyi shiru ana rikici ba

Tsohon shuagaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya bada shawarwari a kan yadda za a shawo kan rikicin makiyaya a Najeriya.

Bukola Saraki ya fito ya yi magana ranar Lahadi, 24 ga wata Junairu, 2021, a shafinsa na Twitter.

Babban ‘Dan siyasar ya bayyana cewa ya na bin duk abubuwan da suke faruwa na sabani da wa’adi da ta’adi a kan Fulani a jihohin Oyo da Ondo.

Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya bayyana cewa abubuwan da ke aukuwa sun jawo tashin hankali a kasa, don haka ya yi kira ga jama'a su hada-kai.

KU KARANTA: Gwamnatin APC ta gaza - Tsohon Ministan Buhari

Bukola Saraki ya kuma yi tir da yadda masu ta-cewa a kan lamarin su kayi tsit. Ya ce: “Gum din da su ka yi ya na da hadari, ya nuna akwai matsala.”

Saraki yake cewa “Dole mu yi magana a kan tagwayen matsalolin nan; rashin tsaro da rashin zaman lafiya.”, ya bada shawara Buhari ya kira taro, a zauna.

Har ila yau, Saraki ya yi kira ga magajinsa, Ahmed Lawal da takwaransa a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila suyi kokarin ganin sun sa bakinsu.

Saraki ya ce a ajiye sabani: “Ya fi yi mana kyau mu hada-kai yanzu, mu kashe wutar rikicin raba kan jama’a da rashin tsaro, mu yi aikin dinke baraka.”

KU KARANTA: Tsaro: Buhari ya ce a fitar wa ECOWAS $20m

Saraki: Ba daidai ba ne ayi gum yayin da ake samun sabani da Makiyaya a Ondo da Oyo
Bukola Saraki Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

“Wannan lokaci ne da ake bukatar a zauna. Yanzu ba lokaci ba ne da za ayi maganar APC da PDP.”

“Ina kuma kira ga ‘yan siyasa masu harin 2023 domin su karbi mulki, suyi tunanin wace irin kasa suke so su mulka bayan 2023, idan aka cigaba a haka.”

Dazu kun ji cewa kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah tace ta fi jin dadi kafin zuwan gwamnatin nan mai-ci ta shugaba Muhammadu Buhari a 2015.

Kungiyar ta karyata rade-radin cewa Muhammadu Buhari yana ba su fifiko a kan sauran al'umma.

A wata hira da aka yi da shi, sakataren 'Yan Miyetti Allah na kasa yace makiyaya ba su amfana da mulkin Buhari ba sai karin makiya da aka jawo masu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng