A Ƙarshe, Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Shirya Yanke Hukunci a Shari'ar Neman Tsige Gwamna
- Kotun daukaka kara ta Abuja ta saurari kararraki hudu da suka shafi sakamakon zaben gwamnan Edo da aka gudanar a 21 ga Satumba 2024
- PDP da dan takararta, Asue Ighodalo, sun bukaci a soke sakamakon, yayin da bangaren APC suka shigar da kara don su kare nasararsu
- Lauyoyin PDP sun ce kotun zabe ta gaza gane yadda rashin lambar SN a fom din EC25B na INEC ya sabawa dokar zabe da aka tanada
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tanadi hukunci kan kararraki uku da kuma wata kara ta daban da aka shigar domin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan Edo.
Masu shigar da karar, suna neman kotun ta soke zaben jihar na ranar 21 ga Satumba, wanda INEC ta ayyana dan takarar APC, Monday Okpebholo, a matsayin wanda ya yi nasara.

Asali: Facebook
Kotu ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben Edo
Kwamitin alkalan kotun mai mutum uku, karkashin jagorancin mai shari’a Mohamed Danjuma, ya ce za a sanar da bangarorin da karar ta shafa ranar da za a yanke hukunci, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin kararrakin da kotun ta saurara akwai wadda jam’iyyar PDP da dan takararta, Asue Ighodalo suka shigar, da kuma wata kara ta daban da APC da Monday Okpebholo suka shigar domin kare nasarar su.
Lauyoyin masu daukaka kara sun roki kotu da ta amince da kararrakin su fi tare da kuma soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta yanke a ranar 2 ga Afrilu.
Lauyan Ighodalo da PDP, Robert Emukpoeruo (SAN), ya bukaci kotu da ta soke hukuncin kotun zaben bisa dalilin cewa kotun ta kasa fahimtar girman zargin rashin gaskiyar da ake yi wa INEC da wadanda ake kara.
PDP ta gabatar da dalilan daukaka kara
Ya ce babu lambar SN a takardar fom din EC25B kamar yadda sashe na 73(2) na dokar zabe ta 2022 ya tanada.
Ya kara da cewa:
"Kotun zabe ta ce sai mun kawo shaidun wakilan rumfuna don tabbatar da yadda aka cike ko aka gaza cike takardun. Amma ba hakan ne manufar shari'ar mu ba. Abin da muke cewa shi ne fom din EC25B ba ya dauke da lambar SN.”
Ya kuma zargi kotun zabe da yin kuskure wajen cewa takardun da suka gabatar an gabatar da su ne ba tare da tsari ba, yana mai cewa irin karar da suka shigar ba ta bukatar irin wannan tsari.
Emukpoeruo ya jaddada cewa wadanda yake karewa na kalubalantar zaben saboda rikice-rikicen da suka faru, musamman sabani a sakamakon da aka tattara a mazabu da wanda aka bayyana a ofishin INEC.
A karshe, ya ce daga cikin hujjojin su akwai cewa sakamakon da aka fitar a mazabu ya saba da wanda aka bayyana daga ofishin INEC.

Asali: Facebook
INEC, APC sun nemi kotu ta kori kararrakin
Sai dai lauyoyin wadanda ake kara sun bukaci kotu da ta tabbatar da hukuncin kotun zabe tare da watsi da daukaka kararrakin, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Onyechi Ikpeazu, daya daga cikin lauyoyin, ya bayyana cewa karar da aka shigar da kuma daukaka karar ba su da amfani sai dai don bata lokacin kotu a nazari kawai.
Emmanuel Ukala (SAN) da ke kare APC da kuma Kanu Agabi (SAN) wanda ya tsaya wa INEC, suma sun nemi kotu da ta yi watsi da daukaka karar tare da tabbatar da hukuncin da kotun zabe ta yanke.
Kotun ta kuma saurari wasu karin kararraki guda biyu: Daya daga jam’iyyar AA da shugaban jam’iyyar Rufai Omoaje da kuma wani daga Bright Enabulele da jam’iyyar AP.
Kotu ta kori karar AA kan zaben Edo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a Edo ta yi watsi da karar da jam’iyyar AA ta shigar, na kalubalantar nasarar APC da Monday Okpebholo.
AA ta zargi hukumar INEC da hana 'yan takara sahihin dan takararta tsayawa takara, sai dai kotun ta bayyana cewa batun ya faru ne kafin zabe, don haka ba ya cikin huruminta.
Bayan korar karar jam’iyyar AA da ta jam’iyyar Accord (AP), kotun ta ce za ta mayar da hankali kan karar da jam’iyyar PDP da Asue Ighodalo suka shigar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng