Ministan Buhari Ya Faɗi Dalilin Ɓaɓewarsa da Sule Lamido yayin da Suke Gwamnoni
- Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa shi da Sule Lamido sun yi abota mai karfi lokacin da suka gwamnoni
- Amaechi ya ce sun rabu ne bayan Sule ya yanke shawarar shiga jam’iyyar SDP, maimakon su zauna a APC kamar yadda suka yarda
- Ya ce ya dauka tsohon ministan harkokin wajen yana da ra’ayin sauyi kamar shi, amma daga baya ya fahimci bambanci a siyasarsu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri a mulkin Muhammadfu Buhari, Rotimi Amaechi ya tuna alakar da ke tsakaninsa da Sule Lamido.
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi ya bayyana dalilin da ya sa suka rabu da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.

Asali: Facebook
Amaechi ya fadi haka yayin wata tattaunawa a Abuja ranar Talata, a wajen gabatar da tarihin rayuwar Sule Lamido mai suna 'Being True to Myself', cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lokacin da Amaechi, Sule suka yi mulki
Sule Lamido da Amaechi sun yi mulkin jihohinsu ne na Jigawa da Rivers daga shekarar 2007 zuwa 2015 karkashin PDP.
Sai dai kafin kammala wa'adinsa a 2015, Amaechi ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan hadaka da sauran jam'iyyun adawa a wancan lokaci.
Bayan Muhammadu Buhari ya yi nasarar zama shugaban kasa karkashin APC a 2015, ya ba Amaechi mukamin ministan sufuri.
Shi kuwa Sule Lamido ya ci gaba da kasancewa a jam'iyyar PDP har zuwa yanzu da take adawa a Najeriya.

Asali: Facebook
'Dalilin ɓaɓewa ta da Sule Lamido' - Amaechi
Amaechi ya tuna da zamanin da suke tare da kuma abubuwan da suka sa aka samu sabani da dattijo kuma jigon PDP.
Tsohon ministan wanda ya shugabanci kungiyar gwamnoni lokacin wa'adin Sule na biyu, ya ce lokacin nasu cike yake da zama tsayin daka da bin gaskiya da rikon amana.
Ya bayyana cewa sun yi aiki tare sosai lokacin suna gwamna kuma suna da irin ra'ayi daya har sai da manufofin siyasa suka fara bambanta su.
Ya ce:
“Mun kasance abokai sosai a gwamnati. Mun fuskanci lokutan sabani inda ba mu jitu ba."
Ya kara da cewa ya yi kuskuren daukar Lamido a matsayin mai son sauyi kamar shi, kuma saboda haka ya dinga dogara da shi wajen yanke matakan sauyi.
A cewarsa, Lamido ya yanke shawarar shiga jam’iyyar SDP wanda hakan ne sanadin da ya lalata hadin kansu, TheCable ta ruwaito.
Ya kara da cewa:
“Mun ce, ‘Idan muka shiga SDP, za mu fadi zabe, mu tsaya a nan cikin APC, amma ya ki amincewa, ya bar mu, a nan ne muka rabu,”
'Amaechi ne ya dace da Najeriya' - Jigon APC
Kun ji cewa jigon APC a jihar Rivers, Eze Chukwuemeka Eze ya ce ƴan Najeriya sun fara rokon tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya fito takarar shugaban kasa.
Mista Eze ya bayyana Amaechi a matsayin mutum mai nagarta wanda ya dace da shugabancin Najeriya a 2027 a halin da ƙasar ke ciki.
Jigon APC ya kuma soki gwamnatin Bola Tinubu saboda yadda ta maida hankali wajen shirin zaɓe maimakon magance damuwar talakawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng