Amaechi Ya Tuna Alakarsa da Sule Lamido, Ya Fadi Abin da Za Su Yi Wa Tinubu da Suna Gwamnoni
- Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda al'amura suke tafiya a siyasar Najeriya a mulkin APC
- Amaechi ya bayyana cewa da da a ce da shi da Sule Lamido suna gwamnoni, da sun ƙalubalanci gwamnati kan yadda abubuwa suke tafiya
- Tsohon gwamnan ya nuna cewa a lokacin da suka yi mulki a jihohinsu, sun tsaya tsayin daka wajen ganin gwamnati ta yi abin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya tuna baya musamman game da alaƙarsa da Sule Lamido.
Rotimi Amaechi ya ce da shi da Sule Lamido ba za su lamunci halin da Najeriya ke ciki a yanzu ba, da ace har yanzu suna kan mulki a matsayin gwamnonin jihohi.

Asali: Facebook
Amaechi ya yi jawabi a bikin littafi Sule Lamido
Rotimi Amaechi wanda tsohon ministan sufuri ne, ya yi wannan jawabi ne a Abuja ranar Talata, a wajen kaddamar da littafin tarihin rayuwar Sule Lamido mai suna 'Being True to Myself', cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amaechi, wanda ya shugabanci ƙungiyar gwamnonin Najeriya a lokacin wa'adin Sule Lamido na biyu a matsayin gwamnan Jigawa, ya ce lokacin mulkinsu lokaci ne na kishin ƙasa da tsayawa tsayin daka wajen tilastawa gwamnatin tarayya yin abin da ya dace.
"Na tambaye ka (Lamido) da safe yau, abin da ke faruwa a ƙasar nan yanzu, a harkar siyasar Najeriya, da ace hakan zai iya faruwa a lokacin da muke gwamnoni? Ka ce a'a. Kuma gaskiya ce. Amsar ita ce a'a.”
"Da mun fuskanci gwamnati, da mun ƙalubalanci shugaban ƙasa. Haka ka ke da tsauri. Haka ƙungiyar gwamnoninmu ke aiki a wancan lokacin. Haka muka ƙudiri aniyar kawo sauyi.”
- Rotimi Amaechi
Dangantakar Rotimi Amaechi da Sule Lamido
Rotimi Amaechi ya yi tsokaci kan dangantakar siyasarsa da Sule Lamido, inda ya ce ko da yake suna kawance a lokacin da suke kan mulki, ra'ayinsu ya bambanta dangane da dabarar adawa da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana kyakkyawar alaƙa da Sule Lamido a lokacin da suke gwamnati, rahoton The Punch ya tabbatar.

Asali: Twitter
"Mun kasance abokai sosai a lokacin gwamnati. Mun samu matsaloli a lokacin da muka saɓa ra’ayi."
"Na yi kuskuren daukar shi tamkar yana da tsaurin ra’ayi kamar ni. Shi ya sa ya kasance daya daga cikin gwamnonin da na jingina da su a lokacin da ake yanke matakai masu tsauri.”
"Na ƙarshe kafin mu rabu shi ne lokacin da muka yanke shawarar mu yi adawa da Shugaba Jonathan. Mun kafa kwamiti na gwamnoni da wasu."
"A ƙarshe kuwa, sai ya tafi ya nemo sabuwar jam’iyya, wato SDP. Mun ce, ‘Idan muka tafi SDP, za mu faɗi zabe. Mu dai mu tsaya a wannan mai suna APC.’ Ya ƙi yarda da hakan ya bar mu. A nan ne hanyoyinmu suka rabu."
- Rotimi Amaechi
Sule Lamido ya roƙi alfarmar Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya miƙa buƙatarsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Sule Lamido ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya biya MKO Abiola bashin N45bn da ya biyo gwamnatin tarayyya.
Tsohon gwamnan ya nuna cewa yin hakan zai sanya a rufe babin zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993 da ake cece-kuce a kai.
Asali: Legit.ng