Bayan Kalaman El Rufai game da Komawa SDP, Buhari Ya Fadi Matsayarsa a APC
- Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa har yanzu shi 'dan jam’iyyar APC kuma yana son a rika kiransa da hakan
- Muhammadu Buhari ya ce ba zai taba juyawa jam’iyyar baya ba, domin ita ce ta ba shi damar shugabanci kasar nan har sau biyu
- Ya ce ya na matukar godiya da irin goyon bayan da APC ta ba shi tun kafin ya zama shugaban kasa har zuwa karshen mulkinsa
- Buhari ya jinjinawa wadanda suka kafa jam’iyyar, ya ce sadaukarwar da suka yi domin kare dimokuradiyya na da matukar muhimmanci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan matsayarsa game da jam'iyyar APC.
Buhari ya sake jaddada cewa har yanzu shi mamba ne na jam’iyyar kuma yana so a kira shi da hakan.

Asali: Twitter
El-Rufai ya fadi yadda suka yi da Buhari
Hadimin Buhari a bangaren sadarwa, Garba Shehu shi ya bayyana hakan a yau Alhamis 13 ga watan Maris, 2025 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan kalaman Nasir El-Rufai da yake fadin yadda suka yi da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a gidansa kafin komawa SDP.
Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa da sanin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya fice daga APC zuwa SDP.
El-Rufai ya ce ya je har gida, ya faɗa wa Buhari cewa ga shirin da yake yi na barin APC kuma ya amince da hakan.
Tsohon gwamnan ya ce Buhari ne mai gidansa na farko a siyasa kuma ba ya ɗaukar kowane irin mataki tun yana gwamna sai ya tuntuɓe shi.

Asali: Twitter
Buhari ya fadi matsayarsa game da APC
Tsohon shugaban ya ce yana so ya tabbatar wa kowa cewa ba zai taba juya wa jam’iyyar baya ba, wadda ta ba shi damar mulki sau biyu.
Buhari ya ce:
“Ni mamba me na APC kuma ina son a rika kirana haka, zan yi iya kokarina wajen tallata jam’iyyar ta kowane hali.”
Ya kara da cewa a yanzu babu abin da yake da shi sai godiya ga goyon bayan da jam’iyyar ta ba shi kafin da lokacin mulkinsa.
Buhari ya ce wannan goyon bayan da ya samu a matsayin shugaban kasa, shi ne mafi girma a rayuwarsa, kuma ba zai bukaci wani abu fiye da haka ba.
Ya bayyana cewa wahalhalun da wadanda suka kafa jam’iyyar suka sha don samar da tsayayyen tsarin kare kundin tsarin mulki da dimokuradiyya abin yabo ne.
Sowore ya zargi Buhari da kisan gilla
Kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya zargi Nasir El-Rufai da hannu a kisan fiye da 'yan Shi’a 300 a 2015.
Omoyele Sowore ya bukaci a gurfanar da El-Rufai, Muhammadu Buhari da Tukur Buratai a gaban kotun ICC saboda zargin laifuffukansu.

Kara karanta wannan
El Rufai ya bayyana yadda suka yi da Buhari kan batun ficewarsa daga APC zuwa SDP
Ɗan gwagwarmaya kuma 'dan siyasar ya caccaki masu murna da sauya shekar da El-Rufai ya yi daga jam’iyyar APC zuwa SDP mai adawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng