Gwamna Fintiri Ya Kawo Karshen Jita Jita kan Shirin Ficewa daga PDP

Gwamna Fintiri Ya Kawo Karshen Jita Jita kan Shirin Ficewa daga PDP

  • Mai girma Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya musanta cewa yana da shirin ficewa daga jam'iyyar PDP
  • Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa Gwamna Fintiri zai tattara ƴan komatsansa daga PDP
  • Domin kashe rade-radin da ake ji, ya bayyana cewa gwamnan ya maida hankali ne wajen sauke nauyin da aka daura masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi magana kan shirin ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Gwamna Fintiri ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo kan cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar PDP.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
Gwamna Fintiri ya ce bai da shirin ficewa daga PDP Hoto: @GovernorAUF
Asali: Facebook

Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya ƙaryata jita-jitar yayin ganawa da manema labarai a ƙarshen mako, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Humwashi Wonosikou ya jaddada cewa Gwamna Fintiri har yanzu ɗan jam’iyyar PDP ne na gaskiya kuma mai kishin ta.

Guguwar sauya sheƙa na gigita PDP

Jam’iyyar PDP dai na fuskantar ficewar manyan ƴan siyasa zuwa APC, musamman a yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen 2027.

Ficewar gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, daga PDP zuwa APC ita ce ta kwana-kwanan nan cikin jerin sauya sheƙar ƴan adawa zuwa jam’iyya mai mulki.

Gwamna Oborevwori ya sauya sheƙa zuwa APC tare da tsohon gwamnan jihar Delta kuma abokin takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban ƙasa na 2023, Ifeanyi Okowa, da kuma gaba ɗaya tsarin jam’iyyar PDP na Delta.

Da yake karɓar masu sauya sheƙar, shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar za ta karɓi ƙarin wasu gwamnonin PDP nan gaba kaɗan.

Me Gwamna Fintiri ya tasa a gaba?

Da yake magana a lokacin ganawa da manema labaran da aka gudanar a Yola a ƙarshen mako, Wonosikou ya bayyana cewa gwamnan ya maida hankali kan sauke nauyin da PDP ta ɗora masa.

Ya bayyana cewa a yanzu Gwamna Fintiri ya maida hankali ne kan gudanar da ayyukansa a matsayin shugaban kwamitin shirya babban taron ƙasa na jam’iyyar PDP.

Ahmadu Umaru Fintiri
Gwamna Fintiri ya karyata jita-jitar shirin ficewa daga PDP Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Twitter

Sakataren yaɗa labaran ya ba da tabbacin cewa gwamnan bai da shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.

“Ina tabbatar muku cewa mai girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri har yanzu ɗan jam’iyyar PDP ne na gaskiya. Ba zai bar jam’iyyar ba."

- Humwashi Wonosikou

Ganawa da manema labaran wadda ta haɗa ƴan jarida da jami’an yaɗa labarai na gwamnati, ta kasance wata dama ta duba nasarorin da gwamnatin Gwamna Fintiri ta cimma a watanni ukun farko na shekarar 2025.

Fintiri a siyasar Adamawa

A siyasance, Ahmadu Umaru Fintiri na daga cikin matasan shugabanni da suka fara bayyana a tsakiyar shekarun 2000 da sabuwar manufa ta shugabanci.

A matsayinsa na tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Adamawa kuma wanda ya taka rawar gani a matsayin mukaddashin gwamna kafin daga bisani ya ci zaɓe a matsayin gwamna, Fintiri ya sha sauya fasalin gwamnati a jiharsa.

Ana masa kallon daya daga ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan kabilu, musamman a yankin Arewa maso Gabas wanda ke fuskantar kalubalen tsaro da koma-baya na tattalin arziki.

A lokacin da dimokuraɗiyyar Najeriya ke fuskantar cikas daga sauya sheƙar ’yan siyasa da rashin daidaito cikin jam’iyyun siyasa, kasancewar Fintiri yana nan daram cikin jam’iyyarsa alama ce ta daidaiton hali da kishin jam’iyya.

Wannan ya ƙara jaddada matsayin Adamawa a matsayin wata muhimmiyar jihar adawa a shiyyar Arewa maso Gabas.

Akwai kuma waɗanda ke ganin irin wannan nagarta tana da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa jam’iyyar PDP a yankin, musamman yayin da wasu jihohi ke fama da rugujewar tsarin cikin gida.

Wannan biyayya da kwarin gwiwa na Fintiri zai iya zama jigon sake farfaɗo da jam’iyyar PDP a matakin ƙasa, musamman gabanin babban zaɓen 2027.

Gwamna Fintiri ya dakatar da basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ɗauki matakin ladabtar da wani basarake.

Gwamna Fintiri ya dakatar da Sarkin Daware, Alhaji Hassan Jafaru, har sai baba ta gani saboda wasu zarge-zarge da ake yi masa.

Dakatarwar da aka yi wa basaraken ta biyo bayan binciken da aka gudanar a kansa, aka same shi da laifi kan zarge-zargen da ake yi masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng