Makwanni da Yin Ritaya, Babban Ɗan Sanda Ya Shiga APC, Zai Nemi Takarar Sanata
- Tsohon mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Ari Muhammed Ali, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC bayan ritaya, zai nemi kujerar Sanata a 2027
- An kori Ari tare da wasu manyan jami’ai saboda zargin sauya shekarun haihuwa da karya ka’idojin aiki, karkashin IGP Kayode Egbetokun
- Wata majiya ya bayyana cewa Ari zsi nemi kujerar Sanata a Nasarawa ta Kudu, yana bi sahun tsohon IGP, Mohammed damu da ke neman gwamna a jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Rahotanni sun ce tsohon mataimakin Sufeto-Janar na rundunar 'yan sanda, DIG Ari Muhammed Ali, ya shiga jam’iyyar APC.
An tabbatar da Ari Muhammad ya koma APC ne makwanni kadan bayan yin ritaya kuma yana son neman kujerar Sanata a zaben shekarar 2027.

Asali: Facebook
Tsohon ɗan sanda zai nemi takarar Sanata
Rahoton Sahara Reporters ya ce Muhammad Ari ya shiga jam'iyyar APC e bayan ya yi ritaya a watan Maris din shekarar 2025 da ta wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kori DIG Ari Muhammed daga aiki karkashin jagorancin Sufeto Janar Kayode Egbetokun, wanda shima ake sukar kin yin ritaya daga aikin dan sanda.
An kori Ari da wasu DIGs Dasuki Galandachi, Rhoda Adetutu Olofu, Jonathan Towuru, Suleiman Yusuf, Banji Lawal Badru da Bala Ciroma kan wasu zarge-zarge.
Majiyoyi sun ce cewa Ari ya shiga APC, yana kuma fatan lashe kujera a Majalisar Dattijai a zabukan 2027.
Wata majiya ta ce:
"Ari Mohammed shi ma yana neman kujerar Sanata a Nasarawa ta Kudu a karkashin APC."

Asali: Getty Images
Tsofaffin ƴan sanda sun dawo siyasa
Ari ta bi sahun tsohon Sufeto-Janar, Mohammed Adamu, wanda bayan ritaya a 2021, yana son zama gwamna a jihar.
An ruwaito cewa Adamu ya bayyana kudirinsa na neman kujerar gwamna na Nasarawa a zaben 2027 a karkashin APC.
Adamu, wanda ya jagoranci ‘yan sanda daga 2019 zuwa 2021 a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya bayyana hakan yayin taro da shugabannin APC a Lafia.
Tsohon Sufeto Janar ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan “kiran gaggawa” daga jama'ar jihar Nasarawa masu bukatar shugabancinsa.
An tabbatar da shigan Ari Mohammed APC
Wani matashi mai suna Abdulmalik Mohammed ya tabbatar da rahoton shigan Ari jam'iyyar APC mai mulkin jihar a shafinsa na Facebook.
A rubutunsa ya ce:
"Kwanaki kadan bayan ya yi ritaya, mataimakin shugaban yan sandan Najeriya, DIG Ari Muhammad Ali ya fada Jam’iyyar APC.
"Ya kuma bayyana bukatar tsayawa takarar Sanata a mazabar Nasarawa ta Kudu."
Gwamna Sule ya musanta zaben maganinsa
Kun ji cewa Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya fito ya yi magana kan batun cewa ya zaɓi wanda zai gaje shi a shekarar 2027.
Gwamna Sule ya musanta cewa ya zaɓi wani ɗan takara da zai gaje shi idan ya kammala wa'adinsa karo na biyu.
Ya buƙaci mutanen jihar da su yi watsi da jita-jitar, ya ce zai ci gaba da ayyukan raya ƙasa kafin ya bar kan kujerar mulki.
Asali: Legit.ng