2027: An Kitsawa Gwamnan PDP yadda Zai Mori Tinubu ba tare da Komawa APC ba
- Kungiyar 'Osun Leaders of Thought' ta bukaci Gwamna Ademola Adeleke da ka da ya bar PDP duk da matsin lamba daga wasu bangarori
- Ta shawarci Adeleke ya marawa shugaba Bola Tinubu baya a zaben 2027, saboda dangantakar jin kai da ke tsakanin Osun da shugaban kasa
- Osun Leaders of Thought ta ce komawa APC za ta haifar da rikici a siyasar Osun, kuma hakan zai kawo cikas ga mulkin Tinubu da Adeleke
- Ta kuma bukaci a cimma yarjejeniya tsakanin Shugaba Tinubu da Adeleke ba tare da sauya sheka ba, don kwanciyar hankali a jihar Osun
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Kungiyar 'Osun Leaders of Thought' (OLT) ta ba Gwamna Ademola Adeleke shawara kan zaben 2027.
Kungiyar ta bukaci Gwamna Adeleke da ka da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, amma ya goyi bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Asali: Twitter
A cikin wata sanarwa daga shugaban kungiyar, Adesola Adigun ya fitar ya ce akwai a dalilai da ya sa Adeleke bai kamata ya bar PDP ba, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto ya yi hasashe game da gwamnonin PDP
Wannan na zuwa ne bayan shugaban coci na INRI, Rabaran Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa gwamnoni hudu na PDP za su mara wa APC baya a zaben 2027.
Fasto Ayodele ya bayyana jihohin Akwa Ibom, Enugu, Oyo da kuma jihar Osun a matsayin wadanda za a shawo kansu su sauya zuwa APC.
Malamin ya ce babu wani abu da ake kira kungiyar PDP yanzu, domin dukkan gwamnoni za su yi aiki ne da APC ba tare da wata matsala ba.

Asali: Twitter
2027: Matsin lambar da gwamna Adeleke je fuskanta
Kungiyar ta ce ta lura akwai matsin lamba da Gwamna Adeleke ke fuskanta domin sauya sheka zuwa APC.
A cewar sanarwar:
“Mun lura da karuwar matsin lamba daga wurare daban-daban na ganin Gwamna Adeleke ya sauya sheka zuwa APC, Wannan ba daidai ba ne kuma babu bukatar hakan.
“Mun kuma bukaci Gwamna da ya marawa Shugaban Kasa baya wanda shi ma ya fito daga Osun, kuma dole mu tallafi namu koda me ke faruwa.
“Ga Shugaban Kasa, Gwamna, da masoyansu, muna jaddada cewa sauya sheka zai haifar da matsala a tsakaninsu, zai janyo cikas a Aso Rock da Abere.
Har ila yau, ta ce domin nasara, dole ne a ci gaba da amfani da wannan karbuwa da gwamnan ke da shi a jiharsa, cewar Daily Post.
Ɗan majalisar wakilai ya koma APC a Osun
A baya, mun ba ku labarin cewa dan majalisar wakilai daga jihar Osun, Hon. Oluwole Oke, ya fice daga jam’iyyar PDP bayan shekara 24 yana wakiltar mazabarsa.
Hon. Oke ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan tuntubar abokan siyasarsa, duk da cewa bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga ba.
Rahotanni daga yankin Kudu maso Yamma sun ce Oke na da burin tsayawa takarar mataimakin gwamna a 2026 ko neman kujerar sanata a 2027 karkashin jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng