Rivers: Shugaban Riko Ya Yi Magana kan Batun Fara Bincikar Gwamna Fubara

Rivers: Shugaban Riko Ya Yi Magana kan Batun Fara Bincikar Gwamna Fubara

  • Gwamnatin jihar Rivers ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ta gayyaci dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa
  • Shugaban riƙon ƙwarya na jihar, Ibok-Ete Ibas ya ƙaryata rahotannin, ya ce babu ƙamshin a gaskiya a cikin zancen neman Fubara da Ngozi Odu
  • A cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, an buƙaci jama'a da su yi watsi da rahotannin da suka fara karade gari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Shugaban riƙo ƙwarya na jihar Rivers, Ibok-Ete Ekwe Ibas, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya gayyaci Gwamna Siminalayi Fubara domin ya gurfana a gaban shi.

Ibok-Ete Ekwe Ibas ya ƙaryata rahotannin cewa ya gayyaci gwamnan da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.

Gwamnatin Rivers ta musanta gayyatar Fubara
Ibok-Ete Ibas ya musanta gayyatar Gwamna Fubara Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jihar Rivers, Dede Friday ya fitar a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yaɗa batun gayyatar Gwamna Fubara

A ranar Talata, wasu rahotanni sun bayyana cewa shugaban riƙon ƙwaryar ya gayyaci Gwamna Fubara domin bayyana a gaban kwamitin bincike dangane da naɗin mukamai da ya yi kafin dakatarwar da aka yi masa.

Idan ba a manta ba dai shugaban kasa Bola Tinubu ne ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers a ranar 18 ga watan Maris, saboda rikicin siyasa da ya daɗe yana faruwa a jihar.

Tinubu ya dakatar da Fubara, Ngozi Odu da dukkan ƴan majalisar dokokin jihar Rivers na tsawon watanni shida.

Shugaban ƙasar ya kuma naɗa Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon babban hafsan rundunar sojojin ruwa, a matsayin wanda zai jagoranci harkokin mulki a jihar.

Me gwamnatin Rivers ta ce kan gayyatar Fubara?

A sanarwar da Dede Friday ya fitar, ya bayyana rahotannin da ake yaɗawa a matsayin tsantsagwaron ƙarya, rahoton The Punch ya tabbatar.

Ibok-Ete Ekwe Ibas
Shugaba Tinubu ya nada shugaban riko a Rivers Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter
"Gwamnatin jihar Rivers ta samu labarin wata sanarwa ta bogi da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wacce aka ce ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jiha (SSG)."
"Waɗannan ƙirƙirarrun labarai na bogi an tsara su ne domin yaudarar jama'a, tayar da hankula, da kuma kawo ruɗani a cikin jihar Rivers."
"Ɗaya daga cikin irin wannan sanarwa ta bogi na cewa wai an gayyaci mai girma Gwmana Sir Siminalayi Fubara, GSSRS da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Nma Odu, zuwa taro a gidan gwamnati a ranar Juma’a, 18 ga watan Afrilu, 2025."
"Gwamnatin jihar Rivers na ba da cikakken tabbacin cewa wannan sanarwar ƙarya ce kuma ba ta fito daga wata majiya ta hukuma ba."

- Dede Friday

Dede Friday ya buƙaci jama’a da su yi watsi da rahotannin, yana mai cewa ƙarya ce da masu neman tayar da hankali ke amfani da ita domin tada zaune tsaye a jihar.

Shugaban riƙo a Rivers ya yi naɗe-naɗe

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban riƙo na gwamnatin jihar Rivers, Ibok-Ete Ekwe Ibas ya yi naɗe-naɗe a gwamnatinsa.

Ibok-Ete Ekwe Ibas ya naɗa shugabannin riƙo a ƙananan hukumomi 23 na jihar domin kula da harkokin mulki.

Shugaban riƙon ya kuma dawo da wasu hukumomi da kwamitocin da aka dakatar a lokacin mulkin Gwamna Siminalayi Fubara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng