Legas: Bayan Tsawon Watanni 2, Kotu Ta Yi Hukunci kan Tsige Kakakin Majalisar Dokoki
- Duk da ya koma kan kujerarsa, babbar kotun Legas ta ce sauke Mudashiru Obasa daga matsayin kakakin majalisar dokoki ya saɓa doka
- A watan Janairu, 2025 ne ƴan Majalisar dokokin jihar suka tsige Obasa tare da maye gurbinsa da mace watau Rt. Hon. Mojisola Meranda
- Wannan lamari dai ya haifar da rikici mai tsanani a Majalisar jihar Legas har sai da shugabana ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Babbar Kotun Legas da ke zama Ikeja ta yanke hukunci kan halascin tsige Rt. Hon. Mudashiru Obasa daga matsayin kakakin Majalisar Dokokin Jihar.
Kotun ta ayyana tsige Obasa da aka yi a watan Janairu a matsayin ba bisa ka’ida ba, ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma bai halatta ba.

Asali: Facebook
Premium Times ta ruwaito cewa babbar kotun Legas ta yanke wannan hukuncin ne a ƙarar da aka shigar gabanta kan tsige Obasa, a zamanta na yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta ce an saɓa doka a tsige Obasa
Har ila yau, kotun ta soke duk wani zama da kudurori da aka yanke a ranar 13 ga Janairu, ranar da aka tsige Obasa daga mukaminsa, cewar rahoton Vanguard.
Majalisar dokokin Legas ta sha fama da rikici a kwanakin baya kan tsige Rt. Hon. Obasa da maye gurbinsa da Hon. Meranda.
Idan za ku iya tunawa Obasa ya dawo kujerarsa a watan Maris bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani don sasanta rikicin Majalisar Dokokin Legas.
Sai dai kafin hakan, Hon Obasa ya shigar da kara yana kalubalantar tsige shi da ƴan Majalisa suka yi a watan farko na shekarar 2025.
Ya bayyana Majalisar Dokokin Jihar Legas da Mojisola Meranda, wadda aka nada a matsayin Kakaki bayan tsige shi, a matsayin wadanda ake kara.
Hon. Meranda ta sauka daga mukamin tun a wancan lokaci da Tinubu ya kashe wutar rikicin, wanda hakan ya ba Obasa damar komawa kan kujerarsa.
Rikicin shugaban Majalisar Legas ya zo karshe
Hukuncin kotun na ranar Laraba ya karfafa halaccin dawowarsa kujerar Kakaki, tare da girmama sasancin da shugaban kasa Tinubu ya yi a lokacin da ya sa baki a al’amarin.
Bugu da ƙari, hukuncin da kotun ta yanke yanzu ya tabbatar da halaccin dawowar Obasa kan muƙamiɓsa da kuma warware duk wani shakku da ke tattare da tsige shi.
Ana ganin dai a dokance, hukuncin kotun ya kawo ƙarshen duk wata taƙaddama da saɓanin da ya dabaibaye Majalisar Dokokin Jihar Legas.
Zanga-zanga ta ɓarke a taron APC
A wani labarin, kun ji cewa taron jam’iyyar APC a Legas ya rikida ya zama rikici bayan wasu daga cikin 'ya'yan jam'uyyar sun yi zargin za a ƙaƙaba masu ɗan takara.
An ce wasu daga cikin ƴaƴan APC sun ɓarke da zanga zanga kan abn da suka kira yunƙurin kakakin Majalisar Legas na ƙaƙaba masu ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Ojokoro.
Daya daga cikin masu zanga-zangar, Mista Olusegun Akinoso-Olawaye, ya ce suna zargin jam'iyyar na kokarin kakaba masu ɗan takarar da ba shi da wata alaƙa da yankinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng