Kakakin Majalisar Legas Ta Ji Matsin Lamba, Ta Yi Murabus daga Mukaminta

Kakakin Majalisar Legas Ta Ji Matsin Lamba, Ta Yi Murabus daga Mukaminta

  • Mojisola Meranda ta yi murabus daga mukamin kakakin majalisar Legas yayin da rikicin shugabanci ke ci gaba da rikita siyasar Legas
  • Meranda ta ce ta ajiye mukaminta ne domin kare martabar majalisar, amma hakan ba yana nufin za ta daina fafutukar shugabanci ba
  • Bayan murabus dinta, ‘yan majalisa sun yaba da rawar da ta taka, daga bisani aka rantsar da ita a matsayin mataimakiyar kakakin majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Mojisola Meranda ta yi murabus daga mukaminta na kakakin majalisar Legas, yayin da rikicin shugabanci ke ci gaba da addabar majalisar.

Sai dai rikicin bai kare ba, domin sauke Mudashiru Obasa daga shugabanci ya raba kan ‘yan majalisar da shugabannin jam’iyya a jihar.

Meranda ta yi magana yayin da ta yi murabus daga mukamin shugabar majalisar Legaa
Shugabar majalisar Legas, Mojisola Meranda ta yi murabus daga mukaminta. Hoto: @lshaofficial
Asali: Twitter

TABLE OF CONTENTS

Shugabar majalisar Legas ta yi murabus

Meranda ta ce ta yi murabus ne domin kare martabar majalisar, tare da jaddada cewa ba za ta sauka daga turbar fafutukar shugabanci na-gari ba, inji rahoton Vangaurd.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina ajiye mukamina a matsayin kakakin majalisa," inji Meranda yayin sanar da murabus dinta.

Ta kara da cewa:

"Na san cewa dole ne a wannan mataki, a matsayin shugabarku, in yi wannan sadaukarwa ta yin murabus don kare martabar majalisar."

'Yan majalisa sun yabawa jajircewar Meranda

Kafin ta sanar da murabus, ‘yan majalisa sun yaba da jajircewarta, basirarta da irin rawar da ta taka a dan kankanin lokacin da ta yi a kan mukami.

Desmond Olusola Elliot, daya daga cikin ‘yan majalisar, ya gode mata, yana mai cewa ta nuna kwarewa kuma ta jagoranci majalisar yadda ya kamata.

Wani dan majalisa, Temitope Adewale Ifako-Ijaiye I, ya ce:

"Mun yi murna da irin shugabancinki. Ke gwarzuwa ce a dimokuradiyya. Kin zo, kin yi shugabanci, kuma kin yi nasara."

Bayan murabus din Mojisola Meranda, majalisar ta hanzarta sake tsara shugabancinta tare da yin sababbin nade-nade.

'Yan majalisar Legas sun yabawa Meranda yayin da ta yi murabus daga mukaminta na shugabar majalisar
'Yan majalisa sun fadi abubuwan alheri a kan shugabarsu da ta yi murabus, Mojisola Meranda. Hoto: @lshaofficial
Asali: Twitter

An mayar da David Setonji a matsayin mataimakin babban mai tsawatarwa, sannan Richard Kasumu ya zama mtataimakin shugaban masu rinjaye.

Har ila yau, majalisar ta nada Adewale Temitope a matsayin shugaban masu rinjaye, sannan Mojeed Fatai a matsayin babban mai tsawatarwa.

Meranda ta zama mataimakiyar kakakin majalisa

A wani cigaba da aka samu, an rantsar da Meranda a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar dokokin Legas jim kadan bayan nadinta.

An gudanar da rantsuwar ta ne nan take bayan da 'yan majalisar suka kammala tantancewa da amincewa da sunanta.

Meranda, wacce ta yi murabus a ranar Litinin da rana a matsayin kakakin majalisa, ta amince da mukamin mataimakiyar kakaki tare da alkawarin yi wa jihar hidima da gaskiya.

Duba bidiyon rantsuwar kama aikin da ta yi a kasa:

Jami'an tsaro sun mamaye majalisar Legas

Tun da fari, mun ruwaito cewa, jami’an tsaro sun mamaye harabar majalisar dokokin Legas, suka hana ‘yan jarida shiga zaman da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa zaman zai fara da misalin karfe 1:00 na rana, inda ake sa ran Mojisola Meranda za ta yi murabus daga mukaminta na shugabar majalisar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.