Kwana 1 da Dakatar da Fubara, Gwamna Ya Yi Wa Tinubu Alkawari kan Zaben 2027
- Monday Okpebholo ya karɓi shugabannin kananan hukumomi 17 da suka sauya sheka zuwa APC, ya ce Bola Tinubu zai lashe zaɓen 2027
- Gwamna Okpebholo ya ce gwamnatinsa ta sauya yanayin Edo cikin watanni huɗu, inda ya zargi gwamnatin da ta gabata da lalata jihar
- A ɓangarenta, PDP ta zargi Gwamnan jihar Edo da bai wa masu sauya sheka N2m kowannensu don jawowa jam'iyyar APC goyon baya
- Jam'iyyar ta ce za ta nemi kotun korafin zaben gwamna ta dawo da nasarar Asue Ighodalo a matsayin wanda jama'a suka zaɓa a 2024
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo ya sha alwashin ba Bola Tinubu nasara a zaben 2027 a jihar.
Gwamnan Edo ya fadi haka ne yayin da ya karɓi shugabannin kananan hukumomi 17 daga cikin 18 da suka sauya sheka zuwa APC a birnin Benin.

Asali: Facebook
Gwamna ya karbi ciyamomi zuwa jam'iyyar APC
A wajen taron da aka yi a dakin taro na New Festival, Gwamna Okpebholo ya yabawa shugabancin Bola Tinubu da matakansa, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta rayuwar jama’a, ya ce sun sauya Edo cikin watanni huɗu kacal.
Ya ce:
“Ina maraba da ku shugabanninmu, na yaba da jarumtar ku na ficewa daga jam’iyyarku zuwa APC.
"Wannan matakin yana bukatar ƙwararren ɗan siyasa, da muka karɓi mulki, Edo ba ta tafiya daidai.
"Muna fama da rashin tsaro, kisa, da wawure dukiyar jihar ta hannun masu fakewa da kwangila.”

Asali: Facebook
Gwamna ya ba Tinubu tabbacin nasara a 2027
Gwamnan ya gode wa kansiloli da suka fito da ra’ayoyin al’umma a lokacin cire shugabannin da suka gabata da zaɓen sabbin shugabanni a kananan hukumomi.
Gwamna Okpebholo ya kara da cewa:
“Shekarar 2027 za ta fara a Edo, ku koma yankunanku ku kafa allunan talla don ci gaban Tinubu a matsayin shugaban kasa.
“Babu gurbi a Abuja a 2027, wadanda ke ƙirƙirar jam’iyya yanzu ba za su yi mulki ba, domin sun gagara a jihohinsu.”
Sakataren jam’iyyar APC, Lawrence Okah, ya gode wa sababbin mambobin da suka sauya sheka, yana mai kiran su haɗu da sauran ‘yan jam’iyyar.
Shugaban ALGON da kuma na karamar hukumar Esan ta Tsakiya, Hon. Kelvin Iyere, ya gode wa gwamna da mambobin APC da suka karɓe su cikin jam’iyyar.
Jam'iyyar PDP ta zargi gwamna da raba kudi
A martanin PDP, ta zargi Gwamna Okpebholo da bai wa waɗanda suka sauya sheka N2m don su goyi bayansa, cewar Vanguard.
Chris Nehikhare na PDP ya ce:
“Muna Allah-wadai da amfani da dukiyar jihar don siyan goyon baya, yayin da sassan jihar ke cikin matsaloli da dama.”
Edo: Ƴan majalisa 4 sun koma APC
Kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu rinjaye a majalisar dokokin jihar Edo da mambobinta huɗu suka sauya sheƙa daga PDP da LP zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan
El Rufai ya sake bankado babban lamari, ya zargi Gwamna Uba da 'Satar' kuɗin Kaduna
Ƴan Majalisar sun tabbatar da komawa APC ne yayin da suka kai ziyara sakatariyar jam'iyyar da ke Birnin Benin a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng