Gwamna Ya Gano Badaƙalar Kudi, Ya Dakatar da Kwamishina da Shugaban Hukuma Nan Take

Gwamna Ya Gano Badaƙalar Kudi, Ya Dakatar da Kwamishina da Shugaban Hukuma Nan Take

  • Gwamna Monday Okpebholo ya dakatar da Antoni-Janar na Edo da shugaban hukumar kula da harkokin kananan hukumomi kan zargin rashawa
  • A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Edo, Umar Musa lkhilor ya fitar ranar Laraba, ya ce dakatarwar za ta fara aiki ne nan take
  • Dakataccen kwamishinan shari'a na Edo ya ce babu wanda ya nemi jin ta bakinsa kan zargin aikata rashin gaskiya kafin wannan sanarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya dakatar da Antoni-Janar kuma kwamishinan shari’a, Hon. Samson Osagie, da shugaban hukumar kula da harkokin kananan hukumomin, Hon. Damian Lawani.

Gwamna Okpebholo ya dakatar da waɗannan manyan ƙusoshin gwamnati ne bisa zargin hannu a badaƙalar karkatar da kuɗaɗen baitul-mali.

Gwamna Monday Okpebholo.
Gwamnan Edo ya dakatar da mutum 2 daga aiki kan zargin karkatar da kuɗin gwamnati Hoto: @M_Akpakomiza
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa wannan mataki na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin Edo, Umar Musa lkhilor, ya fitar a daren jiya Laraba.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu, an kori kwamishinoni 3 daga aikin INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya dakatar da jami'ai 2 nan take

Sanarwar ta bayyana cewa matakin da mai girma gwamnan ya ɗauka na dakatar da su zai fara aiki ne nan take har sai an kammala bincike.

"Dakatar da Hon. Damian Lawani da Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a ya zama wajibi don bai wa Gwamnati damar gudanar da cikakken bincike kan zargin cin hanci da ake masu."
"A halin yanzu za su bar ofis bayan dakatar da su har sai an kammala bincike," in ji sanarwar.

Gwamna Okpebholo ya kafa kwamitin bincike

Sakataren gwamnatin Edo ya kara da cewa Okpebolo ya bayar da umarnin kafa kwamitin da zai binciki zargin da ake yi wa manyan jami’an biyu tare da bayar da shawarwarin da suka dace.

Da yake martani, kwamishinan da aka dakatar, Rt. Hon. Samson Osagie, ya musanta cewa yana da hannu a zamba kuma ya sha alwashin kare kansa daga zargin.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a makarantar allo, an samu asarar rayukan dalibai

Kwamishina ya shirya kare kansa

A wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu da kansa domin mayar da martani kan dakatarwar da aka yi masa, Osagie ya ce:

“Na ga wata sanarwa da gwamnati ta fitar ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025 wanda ake zargi na da hannu a badakalar kudi tare da shugaban hukumar ƙananan hukumomi, bisa haka aka dakatar da ni.
"Ina mai tabbatar da cewa babu hannu na a duk wata badaƙalar kudi ko wata mu'amalar kudi ta rashin gaskiya kuma babu wanda ya tuntuɓe ni kan haka kafin dakatar da ni."
"Zan zauna cikin shirin kare kai na kuma zan tabbatar da cewa ba ni da laifi ko kaɗan domin wanke kai na da sunana wanɗa na shafe shekaru ina ginawa," in ji shi.

Gwamnan Edo ya yi wa Tinubu alƙawari

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo ya sha alwashin ba Tinubu duka ƙuri'un mutanen jihar Edo a zaɓen shugbaan ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala

Gwamnan ya ce ba sai an tallata Tinubu ba a jihar Edo domin tallafin da yake rabawa talakawa kaɗai ya isa ya sa mutane su sake ba shi amanar ƙasarsu a karo na biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262