Abin Duniya Ya Damu PDP, Ta Yi Tir da Kwace Filinta da Gwamnatin APC Ta Yi

Abin Duniya Ya Damu PDP, Ta Yi Tir da Kwace Filinta da Gwamnatin APC Ta Yi

  • Jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi Allah-wadai da matakin ƙwace haƙƙin mallakar filayenta da ke zama hedikwatarta a birnin Abuja
  • Sakataren yaɗa labarai na PDP, Hon. Debo Ologunagba, ya zargi APC da ƙoƙarin murƙushe adawa da gudanar da mulkin danniya a ƙasar
  • Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayar da umarnin ƙwace filayen PDP bisa zargin kin biyan haraji na shekaru 20

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi Allah-wadai da kwace haƙƙin mallakar filinta da ke zama hedikwatarta ta ƙasa a Abuja.

Jam’iyyar, wacce Bola Tinubu ya dakatar da gwamnanta a jihar Ribas, ta ce wannan mataki yunƙuri ne na danniyar adawa.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Gwamnonin PDP sun fusata, sun fadi kuskuren Tinubu

Jam'iyya
PDP ta yi tir da kwace ikon mallakar filayenta Hoto: Umar Damagum/Nyesom Wike
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa sakataren yaɗa labarai na ƙasa na PDP, Hon. Debo Ologunagba, ne ya bayyana haka yayin da yake mayar da martani kan kwace filayen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa, baya ga harabar da ake gina hedikwatar na dindindin a Central Area, an kuma kwace haƙƙin filin da ke Wadata Plaza a Wuse Zone 5.

Yadda Ministan Abuja ya kwace filin PDP

Jaridar Punch ta wallafa cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ne ya bayar da umarnin kwace haƙƙin mallakar filayen PDP a Central Area.

Wasikar da Chijioke Nwankwoeze, daraktan kula da filaye a ma’aikatar, ya sanyawa hannu a madadin minista, ta bayyana cewa an kwace filayen ne saboda PDP ta ki biyan haraji na shekaru 20.

Tinubu
PDP ta zargi gwamnatin Tinubu da danniya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Baya ga Wadata Plaza da filin ginin hedikwatar na dindindin, PDP na kuma amfani da Legacy House da ke Maitama wajen gudanar da ayyukanta.

Ana amfani da Wike wajen takura mana – PDP

Kara karanta wannan

'Ka nesanta kan ka da Rivers': PDP ta gargaɗi 'shugaban riƙo' da Tinubu ya nada

Mai magana da yawun PDP, Ologunagba, ya zargi jam’iyyar APC da kokarin murƙushe adawa, musamman PDP.

Ya ce:

“Yunƙurin da gwamnatin jam’iyyar APC ke yi na kwace haƙƙin mallakar filin da PDP ke amfani da shi a matsayin hedikwata, abin Allah-wadai ne.
"Wannan mataki yunƙuri ne na murƙushe ‘yancin adawa a ƙasar nan kuma wata hanya ce ta kafa mulkin danniya.
Hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya. Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na taro a halin yanzu, kuma zan dawo da cikakken martaninmu nan gaba kadan.”

Jam'iyyar PDP ta fusata da dokar ta baci

A baya, kun samu labarin cewa jam'iyyar PDP ta yi watsi da dokar ta-baci da shugaba Bola Tinubu ya ayyana a jihar Ribas, ta na mai cewa matakin da aka dauka ya sabawa dokar kasa.

PDP ta ce dokar ta-baci da aka ayyana a jihar Ribas na haifar da barazana ga dimokuraɗiyya da kuma ‘yancin jama'a, inda ta bayyana cewa wannan mataki na ya saba kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Fubara, Shugaba Tinubu ya naɗa 'gwamnan riko' a jihar Ribas

A cikin sanarwar da Kakakin jam'iyyar PDP, Hon. Debo Ologunagba, ya fitar, jam'iyyar ta bayyana cewa matakin na Tinubu yana cikin yunkuri na murƙushe dimokuraɗiyya da danniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng