Wike Ya Shafe Fuskarsa da Toka, Ya Ƙwace Filin Hedikwatar Jam'iyyar PDP a Abuja
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kwace filin hedkwatar PDP da ke Abuja, ya na mai zargin jam’iyyar da kasa biyan haraji na tsawon shekaru 20
- Hukumar FCTA ta ce PDP ta gaza biyan kudin harajin filin daga Janairu 2006 zuwa Janairu 2025 duk da gargadin gwamnati ta yi wa masu filaye
- Matakin na FCTA ya yi daidai da sashe na 28(5) na dokar mallakar fili, wanda ke bai wa gwamnati ikon kwace filayen da aka ki biyan harajinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kwace filin hedkwatar PDP na Abuja, ya na mai zargin jam’iyyar da kasa biyan harajin filin na tsawon shekaru 20.
A cewar wata takarda da aka fitar ranar 13 ga watan Maris, 2025, jam'iyyar PDP ta kasa biyan kudin haraji na filin daga ranar 1 ga Janairu, 2006 zuwa 1 ga Janairu, 2025.

Asali: Twitter
Wike ya yi amfani da dokar kasa
Daraktan gudanar da kasa na FCTA, Chijioke Nwankwoeze, ya fitar da sanarwar kwace filin a takardar da ya fitar mai kwanan wata 13 ga Maris, 2025, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardar Chijioke Nwankwoeze ta nuna cewa an dauki matakin ne bisa doka, domin jam’iyyar ta saba sharuddan mallakar fili a babban birnin tarayya.
A cikin takardar da ta samu sahalewar ministan Abuja, Chijioke Nwankwoeze ya ce:
"An umarce ni da na sanar da ku cewa ministan babban birnin tarayya, bisa ikon da doka ta ba shi a karkashin dokar kasa, mai lamba 6 ta 1978, Cap. L5, da ke a kundin dokokin Najeriya na 2004, ya kwace duk wata dama da PDP ke da ita a kan fili mai lamba 243 da ke Central Area, Cadastral Zone A00, Abuja."
Shekaru PDP ba ta biya harajin filin ba
Hukumar FCTA ta bayyana cewa an riga an bai wa PDP dama ta biya kudin da ta ke bin gwamnati, amma ta ki yin hakan duk da gargadin da aka sha yi mata.

Kara karanta wannan
Wike ya soke takardun filaye kusan 5000, an fadi sharadin mayar wa jama'a dukiyarsu
Ta ce tun daga shekarar 2023 ta ke bugawa a jaridu da kafafen yada labarai cewa duk masu filaye a Abuja su biya harajin da ake binsu, kafin zuwan irin wannan ranar.
"Wannan hukunci ya biyo bayan saba dokokin mallakar fili da PDP ta yi, musamman rashin biyan kudin da ya kamata a biya tun daga 1 ga Janairu, 2006 har zuwa 1 ga Janairu, 2025.
"Wannan kuwa duk da yadda FCTA ta sha bayar da gargadi ta kafafen yada labarai cewa masu filaye su biya duk wasu kudaden da suke bin gwamnati."
- Inji sanarwar Chijioke Nwankwoeze.
PDP na fuskantar barazanar rasa hedkwatarta
FCTA ta kuma nuna cewa wannan saba doka ya sabawa sashe na 28, sakin layi na 5(a) da (b) na dokar amfani da fili, wadda ke bai wa gwamnati ikon kwace fili daga wadanda suka ki cika sharuddan mallaka.
Tuni dai wannan mataki ya janyo cece-kuce, inda ake ganin PDP na iya rasa hedkwatarta muddin ba ta dauki mataki ba.
Yanzu haka, FCTA na da damar sake raba filin ga wani ko amfani da shi don wata manufar ta daban daban.
Har zuwa yanzu, jam’iyyar PDP ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan batu ba, amma ana sa ran za ta dauki matakin shari’a ko biyan bashin da ake bin ta.
Wike ya soke takardun filaye 500
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan Abuja, Nyesom Wike, ya amince da soke takardun mallakar filaye 4,794 saboda rashin biyan harajin na sama da shekaru 40.
A yankunan Central Area, Garki I da II, Wuse I da II, Asokoro, Maitama, da Guzape, akwai jimillar masu filaye 8,375 da suka kasa biyan harajin ƙasa cikin shekaru 43 da suka gabata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng