Gwamna a Arewa Ya Jika Wa Al'umma Aiki, Ya Kaddamar da Sabon Taken Jihar
- Gwamna Hyacinth Alia na Jihar Benue ya kaddamar da taken jiharsa da sabbin alamomi don karfafa al'adu, asali da alamar tarihi
- Alia ya bayyana cewa wadannan alamomi suna da matukar muhimmanci wajen tallata jihar, janyo hankalin masu yawon bude ido da masu zuba jari zuwa Benue
- Gwamnan ya yaba wa kwamitin da ya tsara alamomin, yana mai cewa sun yi aiki tukuru don tabbatar da sun wakilci tarihinsu da hadin kan al'umma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Makurdi, Benue - Gwamna Hyacinth Alia na Jihar Benue ya kaddamar da sabon taken jiharsa don bunkasa al’adu, asali, da gadon tarihi.
Gwamnan ya bayyana cewa wadannan alamomi na dauke da ainihin kimar al’adar mutanen Benue, kuma suna nuna darajarsu, tarihi da dabi'unsu.

Asali: Twitter
Gwamna ya kaddamar da sabon taken jiharsa

Kara karanta wannan
'Binani ce ta ci zaɓen Adamawa': Hudu Ari ya yi rantsuwa an tilasta shi game da Fintiri
A yayin bikin karshe da aka yi a Makurdi, Alia ya ce zai mika kudiri ga Majalisar Dokoki domin aiwatar da su, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa alamomin na da muhimmanci wajen tallata jihar domin jawo hankalin masu yawon bude ido da masu zuba jari.
Daga yanzu, jihar za ta zama ta musamman tare da samun martaba ta musamman ta hanyar taken jiharta da sabbin alamomi.
Gwamnan ya ce wadannan alamomi ba wai na ado kawai ba ne, amma suna tunatar da jama’a hakkin da ke kansu a kan jiharsu.
“Suna tuna mana da gwagwarmayarmu da nasarorinmu, kuma suna karfafa mana gwiwa mu yi kokari wajen cimma manyan buruka.
“Suna zama alamar hadin kanmu da bambance-bambancenmu, suna tunatar da mu cewa muna da karfi idan mun hada kai.
“Saboda haka, ina kira ga kowa ya rungumi wadannan alamomi cikin alfahari da kuma sha’awa. Mu yi amfani da su don bunkasa al’adar mu.”
- Cewar Hyacinth Alia
Gwamna ya sha alwashin inganta al'umma
Alia ya gode wa kwamitin da ya tsara wadannan alamomi, yana mai cewa sun yi aiki tukuru don cimma wannan buri.
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cigaban jihar ta hanyar yakar koma-baya da gina ingantattun cibiyoyin lafiya da ilimi.
Ya ce gwamnatin ta dauki matakin daukar sababbin malamai 9,700 domin bunkasa ilimi a jihar.
Alia ya ce suna fuskantar matsalolin tsaro kai tsaye, kuma nan ba da dadewa ba za a mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu.
Gwamna ya gargadi masu neman rigima
Kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya gargadi masu neman kawo masa cikas a cikin mulkinsa inda ya ce su yi hakuri sai bayan shekaru takwas.
Gwamna Alia ya bayyana kansa a matsayin gwamnan jihar Benue kadai, yana mai gargadin masu ta da zaune tsaye da su nisanci jihar.
Asali: Legit.ng