Yanzu-yanzu: Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba, ya saya Fom din takaran shugaban kasa N100m

Yanzu-yanzu: Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba, ya saya Fom din takaran shugaban kasa N100m

  • Tshon dan majalisar wakilai, Emeka Nwajuba, ya shiga jerin masu neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
  • Yace wasu matasa yan kungiyar The Project suka hada masa kudin Fam milyan dari
  • ChukwuEmeka Nwajiuba na niyyar takara karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC

Abuja - Karamin Ministan Ilmi, Hanarabul ChukwuEmeka Nwajiuba, ya sayi Fom din takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC N100m.

Nwajiuba ya sayi Fom din ne a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, a hedkwatar uwar jam'iyyar APC dake birnin tarayya Abuja.

Legit ta samu labari ne daga bakin hadimin shugaban majalisar dattawa kan sabbin kafafen yada labarai, Abubakar Siddiq Usman.

A cewarsa, wasu yan Najeriya ne suka hada masa kudi milyan dari kuma suka saya masa Fam din.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Hadimai, Mataimaka, da Mukarraban Gwamnati Buhari 7 da za su tsaya takara

A cewarsa:

"Karamin Ministan Ilimi, Hon. Chukwuemeka Nwajuiba, ya zama mutumin farko da ya sayi Fom na takarar zaben fidda gwanin jam'iyyar APC yayinda wasu yan Najeriya suka tara sama da N100m don saya masa."

Kalli hotunan Fom din:

Yanzu-yanzu: Karamin Ministan Ilmi, Emeke Nwajiuba, ya saya Fom din takara shugaban kasa N100m
Yanzu-yanzu: Karamin Ministan Ilmi, Emeke Nwajiuba, ya saya Fom din takara shugaban kasa N100m Hoto: Abubakar Sidiq Usman
Asali: Facebook

Ba zan yi murabus a matsayin Minista ba, Karamin ministan Ilmi da ya sayi Fom din takara

Emeka Nwajiuba, ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga kujerarsa ba don ya ayyana niyyar takara kujeran shugaban kasa a 2023.

Jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fidda gwaninta ranar 29 da 30 ga Mayu, 2023.

Nwajiuba ya ce ya amince ya yi takara kujeran ne don zama shugaban Najeriya wanda zai cigaba daga inda shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya, rahoton Vanguard.

Ya ce ba zai yi murabus ba sai ana sauran kwanaki 30 zabe kamar da kundin tsarin mulkin Najeriya ta tanada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel