Shugaba Tinubu Ya Halarci Wurin Tafsir, Ya Roƙi Musulmi Alfarma a Ramadan

Shugaba Tinubu Ya Halarci Wurin Tafsir, Ya Roƙi Musulmi Alfarma a Ramadan

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci musulmin Najeriya su ƙara dagewa da yi wa ƙasa addu'ar samun zaman lafiya da ci gaba
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƙai guda biyu da ke kawo ci gaban kowace ƙasa
  • Shugaban ƙasar ya yi wannan roƙo ne a wurin taron buɗa baki da wa'azin da ƙaramin ministan lafiya ya shirya a jihar Ogun

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya, musamman Musulmai, da su yi amfani da wannan wata mai alfarma na Ramadan wajen yin addu’o'in zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban ƙasa.

Bola Tinubu ya faɗi haka ne a wurin tafsirin Ramadan da iftar da aka shirya a Ayetoro, hedikwatar ƙaramar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun, a daren Lahadi.

Kara karanta wannan

2027: Minista ya fadi abin da ya kamata Musulmai su yi wa Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya roki Musulmi su dage da yi wa ƙasa addu'a Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

The Nation ta ce a wurin taron, an gudanar da addu’o’i na musamman domin nasarar shugaban kasa, Najeriya, dangin Salako na Ayetoro, da kuma rayukan wadanda suka rasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya buƙaci addu'a a Ramadan

Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa zaman lafiya da hadin kai su ne ginshikin ci gaba da wadata.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su roƙi Allah Ya ba shugabanni ikon gudanar da ayyuka na gari domin ƙasar ta samu ci gaba mai ɗorewa.

A cikin jawabin da Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Ali Pate, ya isar a madadin shugaban kasa, Tinubu ya ce:

"Mu ci gaba da rokon Allah ya yi wa kasarmu albarka. Mu roƙi Allah Ya ba shugabanni ikon yin ayyukan da za su kawo ci gaba ga ƙasa.
"Dole ne mu kasance masu kishi da son zaman lafiya da haɗin kai, domin wadannan su ne muhimman ginshiƙan ci gaban Najeriya."

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: Nasir El Rufai ya fitar da sanarwar ficewa daga APC zuwa SDP

Tinubu ya ja hankali kan falalar azumi

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa wannan wata mai alfarma dama ce ta musamman ga Musulmi da duk ‘yan Najeriya su ci gaba da yin addu’a ga kasa da shugabanni.

Ƙaramin ministan lafiya, Dr. Iziaq Kunle Salako, shi ne ya shirya buɗa bakin da kuma wa'azi domin yin addu'a ga mahaifiyarsa, wacce Alla lh ya yi wa rasuwa kwanan nan.

Bola Tinubu ya ƙara jajantawa minista

Shugaban kasa ya jajanta wa ministan bisa wannan rashi, yana mai cewa ko da mutum yana da shekaru nawa, rasa iyaye abu ne mai matukar wahala.

Ya roƙi Allah Ya gafarta wa mamahiyarsa, ya kuma bai wa danginta ikon jure wannan jarrabawa.

Bola Tinubu.
Bola Tinubu ya ƙara jajantawa ƙaramin ministan lafiya bisa rasuwar mahaifiyarsa Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya kuma bukaci Dr. Salako da ya kasance mai jajircewa bisa irin tarbiyya da nagartattun dabi’u da iyayensa suka koya masa.

"Komai yawan shekarun mutum, rasa iyaye yana da matuƙar wahala. Muna addu’a Allah Ya ba ku haƙuri, kuma halayen kirki da iyayenku suka koyar da ku su zama abin kwantar da hankali a rayuwarku."

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da umarnin daukan matasa aiki a dukkan jihohin Najeriya

Minista ya shirya buɗa baki a gidansa

A wani labarin, kun ji cewa ministan ayyuka, David Umahi ya shirya buɗa baki a gidansa da ke jihar Ebonyi a Kudu.

Sanata David Umahi ya buƙaci al'ummar Musulmi da su ci gaba da yi wa Bola Tinubu addu’a da kuma ba shi cikakken goyon baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262