El Rufai Ya Kawar da Jita Jita, Ya Fadi Dalilin Rashin Halartar Taron APC a Abuja
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya fadi dalilin rashin halartar taron jam'iyyar APC da akaa shirya a birnin Abuja
- El-Rufai ya ce bai halarci taron APC ba saboda ba a sanar da shi da wuri ba inda ya ce ya riga ya shirya tafiya zuwa birnin Cairo
- Taron ƙasa na APC taro ne mai muhimmanci da ke haɗa shugabanni, gwamnoni, da manyan jiga-jigai don tattauna batutuwa
- El-Rufai ya ce Ramadan na gabatowa, ya kuma ce ya riga ya yi tsare-tsaren da kuma jiran matakin da jam’iyyar za ta dauka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci taron ƙasa na jam’iyyar APC da aka yi a Abuja ba.
El-Rufai ya koka kan rashin samun gayyata da wuri game da taron, ya ce ya riga ya shirya barin Najeriya zuwa ketare.

Asali: Twitter
Yadda jiga-jigai suka kauracewa taron APC
A wata hira da Arise TV, El-Rufai ya ce ba a sanar da shi da wuri ba, don haka ya riga ya tsara tafiya zuwa Cairo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce kan rashin halartar taron shugabannin APC na kasa da aka gudanar wanda Bola Ahmed Tinubu ya halarta.
An yi ta yada jita-jita saboda rashin ganin wasu kusoshin APC kamar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i a taron ba.
Taron ƙasa na APC taro ne mai muhimmanci da ke haɗa shugaban ƙasa, mataimakinsa, shugaban jam’iyya, gwamnoni da sauran manyan jiga-jigai.
Wannan taro yana ba shugabannin jam’iyya damar daidaita matsaya kan muhimman batutuwan siyasa kafin su gabatar da su a taron NEC, cewar The Nation.

Dalilin El-Rufai na rashin halartar taron APC
A hirar, El-Rufai ya ce:
“Kash, ba zan halarci taron ba, domin zan tafi Cairo inda nake yawan zama, ban samu sanarwa da wuri ba.”
“Dokar jam’iyyarmu na bukatar a sanar da mu akalla kwana 14 ko 21 kafin irin wannan taro, amma hakan bai faru ba.”
“Na riga na shirya tafiya, kuma abokaina da za su halarta za su ba ni labari. Ba na jin zan rasa wani abu.”
“Ramadan yana gabatowa, na shirya tsare-tsarena, na riga na yi magana a bayyane, yanzu zan jira matakin da jam’iyya za ta dauka, ba lallai ne in halarta ba, ni ba ni kaɗai ne mamban jam’iyyar da ke da korafi ba.”
El-Rufai ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu
Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya sake yin magana, ya fadin ra'ayinsa kan manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa wasu daga cikin manufofin da shugaban ƙasan yake aiwatarwa ba su dace ba ko kaɗan.
Tsohon gwamnan ya soki shirin shigo da abinci daga ƙasashen waje, ya ce hakan hanyar lalata harkar noman cikin gida ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng