Gwamnonin PDP Na Goyon Bayan Takarar El Rufai, Peter Obi a 2027? An Fede Gaskiya

Gwamnonin PDP Na Goyon Bayan Takarar El Rufai, Peter Obi a 2027? An Fede Gaskiya

  • Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP mai adawa ta yi martani kan batun wasu gwamnoninta na goyon bayan takarar wasu daban
  • Gwamnonin sun musanta jita-jitar wacce ke cewa wasu daga cikinta na goyon bayan takarar Nasir El-Rufai da Peter Obi a zaɓen 2027
  • Sun bayyana cewa ɗan takarar jam'iyyar PDP kawai za su marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ke zuwa nan gaba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun yi magana kan jita-jitar cewa wasu daga cikin mambobinsu na goyon bayan takarar Nasir El-Rufai/Peter Obi a zaɓen 2027.

Gwamnonin na PDP sun musanta raɗe-raɗin masu cewa suna goyon bayan tikitin takarar shugaban ƙasa na ƴan siyasan biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Gwamnonin PDP sun musanta goyon bayan El-Rufai, Peter Obi
Gwamnonin PDP sun ce dan takarar jam'iyyar kawai za su goyawa baya a 2027 Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Shugaban gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da darakta janar na ƙungiyar, Dr. Emmanuel Agbo, ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ganduje ya sa lokacin yin jana'izar PDP, ya yi gayyata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emmanuel Agbo ya fitar da sanarwar ne a madadin Gwamna Bala a ranar Asabar, 8 ga watan Maris 2025, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Me gwamnonin PDP suka ce kan takarar El-Rufai/Obi?

Sanarwar ta yi Allah-wadai da wallafa irin waɗannan jita-jitar da aka yi a wasu kafafen watsa labarai.

“Ya zama wajibi ga ƙungiyar gwamnonin PDP, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ta fito fili yi Allah-wadai da babbar murya game da waɗannan jita-jita marasa daɗi da ake yaɗawa."
"Waɗannan mutane waɗanda ba su da kyakkyawar niyya da wakilansu ba za su iya jure irin jajircewar wannan ƙungiya ba, wacce ke ƙalubalantar gazawarsu a fannin shugabanci."
"Ƙungiyar gwamnonin PDP ba ta da wata alaƙa da waɗannan mutane, kuma ba ta da wata damar shiga wata tattaunawa ko amincewa da ƙoƙarin siyar da jam’iyyar PDP ta hannun wasu mutane marasa daraja da ake zargin suna aiki a boye don goyon bayan takarar Nasir El-Rufai/Peter Obi a zaɓen 2027."

Kara karanta wannan

Ana raɗe radin Atiku ya bar PDP, Ganduje da Barau sun sharewa Tinubu hanya a jihohi Arewa 19

"A matsayin jam’iyya mai ƙarfi, dukkan bangarorinta suna ci gaba da ƙoƙarin sulhu da haɗin kai domin ci gaba da nasarorin da aka samu a matakin jihohi don inganta rayuwar al’ummarmu."
"Mun ɗauki alƙawari cewa a shekarar 2027, gwamnonin PDP, a matsayinsu na shugabanni masu biyayya da kishin jam’iyya, za su nuna misali ta hanyar goyon bayan duk wanda ya samu takarar shugabancin ƙasa a PDP.|

- Dr. Emmanuel Agbo

Abdullahi Ganduje ya ce PDP ta mutu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi shaguɓe ga PDP mai adawa.

Ganduje ya bayyana cewa PDP na dab da rugujewa saboda rikicin cikin gida da ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya.

Shugaban na APC ya bayyana cewa suna jin daɗi tare da cin moriyar koma bayan da jam'iyyar PDP take fama da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng