Zargin Lalata: Sanata Natasha Ta Sake Yamutsa Hazo, Ta Yi Magana kan Dakatar da Ita

Zargin Lalata: Sanata Natasha Ta Sake Yamutsa Hazo, Ta Yi Magana kan Dakatar da Ita

  • Natasha Akpoti-Uduaghan ta sha alwashin ci gaba da aiki a matsayinta na sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa
  • Sanata Natasha ta bayyana hakan ne yayin da take martani ga matakin da Majalisar Dattawa ta ɗauka a kanta na dakatar da ita
  • Ta ce wannan dakatarwa da ba zata hana ta ci gaba da aiki a matsayin zaɓaɓɓiyar sanata ba kuma za ta wakilci al'umarta daga nan har 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Senata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana dakatarwar da Majalisar Dattawa ta mata a matsayin zalunci da rashin adalci.

Idan ba ku manta ba, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida bisa karya dokokinta.

Sanata Natasha.
Sanata Natasha ta sha alawashin ci gaba da aiki a matsayin sanatar Kogi ta Tsakiya Hoto: Natasha H. Akpoti
Asali: Facebook

Amma a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, Sanata Natasha ta ce wannan haramtacciyar dakatarwar ba za ta hana ta ci gaba da wakiltar al'ummarta ba.

Kara karanta wannan

Sanatan Katsina ya fusata, ya soki sharadin yi wa Natasha afuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Majalisa ta dakatar da Natasha?

An dakatar da Natasha ne bisa zargin ɓata suna da rashin da’a, bayan wani musayar yawu mai zafi da ta yi da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Rigima ta shiga tsakanin Natasha da Akpabio ne kan batun kujerar zamanta a zauren majalisa dattawan a ranar 20 ga Fabrairu, 2024.

Bayan faruwar haka ne Sanata Natasha ta zargi Akpabio da cin zarafinta ta hanyar neman lalata da ita, amma Shugaban Majalisar ya musanta wannan zargi.

A jawabin da ya yi ranar Laraba, Sanata Akpabio ya ce tun da yake bai taɓa cin zarafin mace ba saboda ba haka mahaifiyarsa ta ba shi tarbiyya ba.

Sai dai Sanata Natasha ta miƙa korafinta a hukumance gaban Majalisar Dattawan, tana mai kafewa kan ikirarinta cewa Akpabio ya neme ta da lalata.

Majalisa ta yi watsi da ƙorafin Natasha

Kwamitin ladabtarwa, ɗa'a da ƙorafe-ƙorafen Majalisa ya yi watsi da ƙorafin da Natasha ta shigar, bisa dalilin cewa ba ta bi ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Natasha ta ja daga, ta nufi kotu kan dakatarwar watanni 6 da majalisa ta yi mata

Bugu da ƙari, kwamitin ya ba Majalisa shawarar dakatar da Natasha, riƙe albashi da alawus dinta da kuma janye jami'an tsaronta.

Bayan ƙaɗa kuri'ar murya, Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni shida a zaman ranar Alhamis, 6 ga watan Maris, 2025.

Sanata Natasha ta mayar da martani

A wani sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook, Natasha ta ce matakin da majalisa ta ɗauka a kanta ba zai rage darajarta a matsayin sanata ba.

Ta ce:

"Saɓanin al’adar shiru, tsoratarwa da ƙoƙarin cin mutuncin wanda ke neman haƙƙinsa; dakatarwar da aka mani a Majalisa ya saɓa wa dokar adalci, daidaito da gaskiya."
"Wannan dakatarwa da ta keta doka ba za ta hana ni ci gaba da aiki a matsayin sanata ba. Zan ci gaba da wakiltar al’ummata da ƙasata cikin kwarewa da ƙwazo har zuwa 2027."

Sanata ya roki a sassauta wa Natasha

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha ta fitar da saƙo mai zafi bayan dakatar da ita a Majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Abba Moro daga jihar Benuwai ya roƙi majalisar dattawa ta sassauta dakatarwar da ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Abba Moro, wanda ya amince Natasha Akpoti-Uduaghan ta saɓa dokoki, ya roƙi majalisa da ta rage wa’adin dakatarwarta daga watanni shida zuwa watanni uku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng