An Bukaci Hukumar EFCC Ta Cafke Nasir El Rufa'i cikin Sa'o'i 72
- Kungiyar Kiristocin ta NCA ta bai wa EFCC wa'adin sa'o'i 72 domin kama tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin almundahanar N423bn
- Kiristocin sun zargi EFCC da gaza daukar mataki duk da yawan koke-koken da aka shigar, tana mai cewa kin aiwatar da hakan zai iya haddasa zanga-zanga
- NCA ta yi nuni da rahoton Majalisar Dokokin Kaduna wanda ya bayyana zargin cin hanci da rashawa a cikin bayar da kwangiloli a lokacin El-Rufa'i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Wata kungiyar Kiristocin Arewa ta bai wa Hukumar EFCC wa'adin sa'o'i 72 domin kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i bisa zargin wawure Naira biliyan 423.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, kungiyar ta ce lokaci ya yi da hukumomin yaki da cin hanci za su dauki mataki kan El-Rufai'i.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya na fuskantar barazana daga Trump, Amurka ta dakatar da ayyukan USAID

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa kungiyar NCA ta fadi haka ne biyo bayan zargin da Majalisar Dokokin Kaduna ta yi a kan tsohon gwamnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufa'i: NCA ta zargi EFCC da gaza daukar mataki
Shugaban NCA, Barista Gideon Jato, da Sakataren kungiyar, Sunday Adoka sun zargi EFCC da gazawa duk da yawan koke-koken da aka shigar a kan El-Rufai.
"Abu ne bayyananne cewa dokokin Najeriya suna fifita wasu mutane tare da muzgunawa wasu,"
"Muna tuna yadda EFCC ta shafe kwanaki tana fafutukar kama tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, bisa korafi da aka shigar a kansa daga wata kungiya a jihar."
- Kungiyar NCA
Rahoton majalisar Kaduna kan El-Rufa'i
A cewar NCA, wani kwamitin majalisar dokokin Kaduna a watan Yunin 2024 ya zargi El-Rufa'i da wasu manyan jami'an gwamnatinsa da cin hanci.
Kungiyar ta ce cikin zargin da aka yi wa El-Rufa'i akwai badakalar kwangiloli da kuma amfani da basussuka na cikin gida da na waje da jihar ta karba.

Kara karanta wannan
Matakin da majalisa ta dauka kan zargin Janar Tchiani game da Lakurawa, tana kokwanto
Rahoton kwamitin, wanda shugabansa, Henry Danjuma, ya gabatar, ya bayyana cewa an samu wasu kwararan hujjoji na cin hanci a sassa daban-daban na ma'aikatu a lokacin El-Rufa'i.
Haka nan, an bukaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan dukkan tsofaffin Kwamishinonin Kudi da Akantocin da suka yi aiki tsakanin 2015 da 2023.
NCA ta yi barazanar yin zanga-zanga
NCA ta gargadi EFCC cewa idan har ba a dauki mataki cikin sa’o’i 72 ba, za ta fara gangamin zanga-zanga a duk jihohin Arewa 19.
The Guardian ta wallafa cewa kungiyar ta ce:
"Idan har ba a dauki mataki ba, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen wayar da kan jama’a kan yadda hukumomin yaki da cin hanci ke nuna sakaci.
"Za mu kuma hada mambobinmu daga jihohin Arewa 19 domin tafiya har zuwa hedikwatar EFCC da Majalisar Dokoki ta Kasa."
El-Rufa'i ya goyi bayan Naja kan Ribadu

Kara karanta wannan
Matasan Arewa sun fadi sunayen 'yan siyasa 3 da ke shirin ruguza gwamnatin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i ya goyi bayan Hajiya Naja'atu Mohammed a kan Nuhu Ribadu.
Hajiya Naja'atu Mohammed ta bayyana a cikin wani bidiyo ta na cewa Ribadu ya taba zargin Bola Tinubu da rashawa a shekarun baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng