"Dalilina na Sukar Bola Tinubu a baya," Hadimin Shugaban Kasa
- Daniel Bwala, mai bai wa Shugaban kasa shawara kan yada labarai da tsare-tsare, ya bayyana abin da ya sa shi sukar Bola Tinubu
- Bwala ya kare kansa, yana mai cewa jam’iyyar adawa tana da hakkin sukar gwamnati mai mulki domin tabbatar da an dora ta kan hanya
- A baya, kafin a nada shi a mukaminsa na yanzu, Bwala ya soki zaben Tinubu, yana mai cewa shugaban ba shi ne halastaccen jagora ba
- Sai da a yanzu, ya bayyana cewa akwai dalilin da ya sa ya samu sauyin ra'ayi a kan gwamntin da ya sha suka da ganin haramtacciya ce
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman a kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ya ce tabbas, ya sha sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a baya.
A cikin hirar da ya yi a ranar Talata, Bwala ya kare kansa, yana mai cewa hakan ya faru ne saboda yana cikin jam’iyyar adawa, PDP ba wani dalili na daban ba.

Asali: Facebook
Arise TV ta wallafa cewa a baya, kafin ya zama hadimin Bola Tinubu, Mista Bwala ya zargi gwamnatin Tinubu da tafka magudin zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Dalilin sukar Bola Tinubu,” Danel Bwala
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Bwala ya ce daya daga cikin ayyukan jam’iyyar hamayya shi ne caccakar gwamnati mai ci, kamar yadda ya ke yi a baya.
A kalamansa:
"Na soki zaben Tinubu da gwamnatinsa a baya saboda ina cikin jam'iyyar hamayya.
"Ayyukan jam’iyyar adawa shi ne su rika sukar gwamnati mai mulki tare da daura mata alhakin aikinta.
Ra’ayina ya canza ne bayan na hadu da Shugaban kasa, kuma ya ga dacewar na zama cikin gwamnatinsa.”
Yadda Bwala ya caccaki shugaba Tinubu
Tun kafin nadinsa, Bwala ya zargi Tinubu da magudi a zaben 2023, yana mai cewa hakan zai haifar masa da matsala domin ba shi ne halastaccen shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan
'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023
A wancan lokaci, Bwala ya ce:
"A halin yanzu, duk da cewa doka na bai wa Tinubu goyon baya har sai an yanke hukunci na karshe daga kotun sauraron kararrakin zabe da kuma kotunan daukaka kara, zai yi fama da matsalar halaccin mulki saboda magudin da ya tafka, har tsawon kwanaki 240 na shugabancinsa."
Bwala ya kuma soki hukumar zabe ta INEC, yana mai cewa ta yi magudi a sakamakon zaben shugabancin kasa.
Ya kara da cewa bai dace a kira Tinubu zababben shugaban kasa ba, ya fi dacewa a kira Tinubu da shugaba da aka nada.
Hadimin Tinubu, Bwala ya soki El Rufa'i
A wani labarin, kun ji yadda Mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya sake sukar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Bwala ya ƙara da cewa kalaman tsohin gwamnan ba sa wani tasiri a kan shugaban kasa, ganin yadda shi Nasir El Rufa'i ba zai iya wani katabus wajen raba Bola Tinubu da kujerarsa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng